Yan Bindiga Sun Sace Mata Mai Shayarwa da Wasu Mutum 4 a jihar Kaduna

Yan Bindiga Sun Sace Mata Mai Shayarwa da Wasu Mutum 4 a jihar Kaduna

  • Ƴan bindiga sun tare matafiya suna kan hanyarsu ta komawa gida daga kasuwa a ƙauyen Iche na ƙaramar hukumar Kagarko a jihar Kaduna
  • Miyagun ƴan bindigan waɗanda suka fito daga ƙarƙashin gada sun yi awon gaba da mutum biyar ciki har da wata mata mai shayarwa
  • Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ba ta ce komai ba dangane da harin wanda ya auku a ranar Lahadi, 22 ga watan Oktoban 2023

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da wata mata mai shayarwa da wasu mutane huɗu da suke dawowa daga kasuwa a ƙauyen Iche da ke ƙaramar hukumar Kagarko a jihar Kaduna, cewar rahoton Daily Trust.

Ƙauyen na Iche dai yana da nisan kilomita biyar daga garin Kagarko, hedikwatar ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Malamar Jami'a a Wani Sabon Hari a Arewacin Najeriya

Yan bindiga sun sace mutane a Kaduna
Yan bindiga sun yi awon gaba da mata mai shayarwa a Kaduna Hoto: theguardian.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya auku

Wani mazaunin garin Yahaya Bala ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar Lahadi, 22 ga watan Oktoba, a lokacin da wadanda abin ya shafa ke dawowa daga kasuwar da ke garin Jere a wata mota ƙirar Golf Volkswagen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ƴan bindigan sun fito ne daga ƙarkashin gadar ƙauyen Iche, inda suka buɗe wuta tare da fasa tayoyin gaba na motar, kafin su fitar da mutanen da ƙarfin tsiya tare da tafiya da su cikin daji.

Ya cigaba da cewa:

"Amma matar da yaronta an sako su ne a wani waje nesa kaɗan daga wajen da aka yi garkuwa da su."

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ba ta ce komai ba dangane da wannan lamarin.

Lamarin rashin tsaro na ƙara ta'azzara a jihar Kaduna inda ƴan bindiga ke cigaba da cin karensu babu babbaka, tare da barazana ga rayuka da dukiyoyin mutane waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba.

Kara karanta wannan

Rayukan Yan Bindiga Masu Yawa Sun Salwanta Bayan Sun Kawo Harin Ramuwar Gayya a Jihar Arewa

Sojoji Sun Halaka Yan Ta'adda Masu Tarin Yawa

A wani labarin kuma, dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar sheƙe ƴan ta'adda masu tarin yawa a wani samame da suka kai musu a jihar Sokoto.

Sojojin sun kai samamen ne a maɓoyar ƴan ta'addan inda suka halaka da yawa daga cikinsu tare da ƙwato makamai masu tarin yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng