Hanya 1 Za a Iya Bi Domin Magance Tashin Dala Inji Tsohon Mataimakin Gwamnan CBN

Hanya 1 Za a Iya Bi Domin Magance Tashin Dala Inji Tsohon Mataimakin Gwamnan CBN

  • Kingsley Moghalu ya na ganin idan dai Najeriya ta dogara da kayan wasu kasashe, tattalin arzikinta ba zai yi kyau ba
  • Tsohon mataimakin gwamnan na bankin CBN ya ce dole a rika fita da kayayyaki zuwa ketare idan dai ana so Dala ta sauka
  • Farfesa Moghalu yake cewa har yanzu bai ga alamar ana yi da gaske domin kayan Najeriya su zagaya kasashen waje ba

Abuja - Tsohon mataimakin gwamna a babban bankin CBN, Kingsley Moghalu ya yi bayani a game da karyewar darajar Naira a kasuwa.

Vanguard ta ce Farfesa Kingsley Moghalu ya yi jawabi wajen taron shekara-shekara da NES ta shirya wannan karo a babban birnin Abuja.

Masanin tattalin arzikin yake cewa kudin kasashen waje za su karye ne kurum idan Najeriya ta koma fitar da kayayyakinta zuwa ketare.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari Ya Yi Ya Jawo darajar Naira ta ke Karyewa a Yau – Sanatan PDP

Bola Tinubu
Kingsley Moghalu ya ba Bola Tinubu shawarar tattalin arziki Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Sai an zauna a kan faduwar Naira

A yayin da yake tofa albarkacin bakinsa a kan faduwar da Naira ta ke yi, Kingsley Moghalu ya ce ya kamata ne a dauki mataki mai dorewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Hanyoyin farfado da Naira na da matsala kuma hadin gambizar abubuwa da yawa ne. Wasunsu masu gajeren zango ne.
Amma bari in fari da masu dogon zango domin mun dade mu na so a farfado da Naira, amma abin ya na ta tabarbarewa.
Yadda za a gyara darajar Naira ita ce Najeriya ta zama kasa mai fita da kaya zuwa ketare."

- Kingsley Moghalu

An kama hanyar karya Dala a Najeriya?

The Cable ta ce tsohon mataimakin gwamnan na bankin CBN ya ce shi a ra’ayinsa, har yanzu ba a kama hanyar cin ma manufar da kyau ba.

Kara karanta wannan

Bashin $3.5bn: Tinubu Ya Fadi Yadda Zai Kasafta Kudaden Don Amfanar Talakawa, Ya Fadi Tsawon Lokacin Biya

Farfesan ya nuna cewa daga cikin matsalolin da ake fama da su shi ne jama’a ba su yarda da Naira ba, an komawa sayen kudin kasashen waje.

A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin, Moghalu ya nanata ra’ayin, yake cewa Naira ba za ta yi daraja ba idan ana kawo kayan ketare.

Ben Murray Bruce ya na ganin laifin gwamnatin Muhammadu Buhari ne ba kowa ba.

$1 ta kai N1, 200 a kasuwar canji

Kakaki a majalisar tarayya, Hon. Philip Agbese ya ce Dr. Yemi Cardoso bai san abin da yake yi a CBN ba, a ra'ayinsa ba a dauki hanyar gyara ba.

An ji cewa kuma majalisa ta aikawa Gwamnan bankin CBN sammaci ganin an cire takunkumin bada dala domin a shigo da kaya daga waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng