Magidanci Ya Salwantar da Ran Matarsa a Jihar Benue
- Wani magidanci a jihat Benue ya aikata aikin ɗana sani bayan ya yi amfani ɗa wuƙa ya halaka matarsa
- Magidancin dai ya daɓa wa matar ta sa wuƙa ne wacce ta yi sanadiyyar mutuwarta bayan sun samu rashin jituwa
- Runɗunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin, amma ba ta bayar da cikakkaun bayanai ba
Jiihar Benue - Wani magidanci ya halaka matarsa ta hanyar daɓa mata wuƙa a ranar Talata, 24 ga watan Oktoban 2023 a jihar Benue.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya auku ne da safiyar ranar Talata, a ƙauyen Korinya da ke cikin ƙaramar hukumar Konshisha ta jihar.
Menene abin da ƴan sanda suka.ce kan lamarin?
Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar Benue, SP Catherine Anene, wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce har yanzu babu cikakkun bayanai saboda tana jiran DPO na Konshisha ya aiko mata da rahoto kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, Anene ta ce an gaya mata cewa magidancin ya samu rashin jituwa ne da matarsa kuma a cikin hakan ya yi amfani da wani abu kamar wuƙa ya caka mata.
Ta ce abin da magidancin ya yi amfani da shi wajen daɓawa matarsa, shi ne ya yi sanadiyar mutuwarta.
A halin da ake ciki kuma, wani mazaunin ƙauyen ya bayyana sunan matar da ta rasu a matsayin Mngsunun, mijin kuma a matsayin Bem Matthew Korinya.
Mutumin ya bayyana cewa lamarin kisan ya jawo cece-kuce a ƙauyen na su.
An daɓa wa ɗaliba wuƙa
Wata ɗalibar kwalejin horas da malamai ta NCE ta gamu da ajalinta bayan wasu miyagu sun daɓa mata wuƙa a jihar Gombe
Wasu miyagu ne dai da ba a san ko su wanenw ba suka je har ɗakin ƙwanan ɗalibar suka daɓa mata wuƙa har lahira a ƙaramar hukumar Billiri ta jihar.
Direba Ya Daba Wa Jami'in LASTMA wuka
A wani labarin kuma, wani direban motar danfo a jihar Legas ya yi yunƙurin halaka jami'in hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas (LASTMA).
Direban dai ya ɗaba wa jami'in wuƙa ne bayan an tarbe shi bisa laifin karyar dokar tuƙi.
Asali: Legit.ng