Majalisar Dattawa Ta Kare Matsayarta Na Siyo Motoci Masu Tsada Ga Yan Majalisu
- Majalisar dattawa ta yi ƙarin haske kan dalilin siyo motocin alfarma ga ƴan majalisu duk da halin matsin tattalin arziƙi da ake ciki
- Majalisar ta yi nuni da cewa tana son siyo.motoci ne masu karko waɗanda za su jure rashin kyawun titunan hanyoyin ƙasar nan
- Batun siyo motocin dai ya fusata ƴan Najeriya da dama waɗanda ke ganin siyo motocin a matsayin ɓarnatar da dukiyar ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT, Abuja - Majalisar dattawa a ranar Talata, 24 ga watan Oktoba, ta bayar da hujjar sayan motocin alfarma ga ƴan majalisa duk da mawuyacin halin da ƴan Najeriya ke ciki na matsin tattalin arziki.
Majalisar ta bayyana cewa tana son siyo motoci ne waɗanda za a daɗe ana mora da kuma iya basu kulawar da ta dace a cikin shekara huɗu, cewar rahoton Premium Times.
Shugaban kwamitin ayyuka na majalisar dattawa, Sunday Karimi, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin tarayya Abuja, rahoton Vanguard ya tabbatar.
A kalamansa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Siyo motocin ya dogara ne kan kwatankwacin ƙwarinsu da kuma yanayin titunan hanyoyin Najeriya. Muna son wani abu da za mu iya amfani da shi har na tsawon shekara huɗu."
"Kuma batun siyan motoci ga majalisar tarayya, kun san lamari ne mai sake tasowa, yana faruwa kowace majalisa, a koda yaushe sai ya auku."
An sama ƴan majalisa na mujiya
Hakazalika ya bayyana yadda hankalin jama'a ya karkata kan batun siyo motocin a matsayin rashin adalci ne saboda lamarin ya fi muni a matakin zartarwa.
Karimi ya ce ministocin da ba a zaɓa ba suna hawa jerin gwanon motoci da dama ba tare da jama'a ko kafafen yada labarai sun sanya musu ido ba.
An dai nuna ɓacin rai kan shirin da majalisar tarayya ta yi na siyan motocin ga mambobinta duk kuwa da halin da tattalin arziƙin ƙasar nan ke ciki.
Majalisa Ta Gayyato Gwamnan CBN
A wani labarin kuma, majalisar wakilai ta gayyaci gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya bayyana a gabanta.
Majalisar ta gayyato Cardoso ne domin ya bayar da bayani kan dalilin cire takunkumin bayar da dala kan wasu kayayyaki 43 da ake shigowa da su ƙasar nan.
Asali: Legit.ng