Jerin Shugabannin Hukumar ICPC 8 da Aka Yi Cikin Shekara 23 a Tarihin Najeriya

Jerin Shugabannin Hukumar ICPC 8 da Aka Yi Cikin Shekara 23 a Tarihin Najeriya

  • Cif Olusegun Obasanjo wanda ya hau mulki a 1999, ya kafa ICPC da nufin hukumar za ta yaki cin hanci da rashawa
  • Daga lokacin da aka kafa hukumar a shekarar 2000 a Najeriya, ta samu shugabanni bakwai daga Mustafa Akanbi
  • Tsohon ‘dan sanda, lauya a bangaren shari’a da alkalin da ya yi ritaya su na cikin rukunin wadanda za su iya shugabanci ICPC

Abuja - Bayan da aka samu daga shafin ICPC ya nuna an kirkiro hukumar ne a ranar 29 ga watan Satumba 2000 a zamanin Olusegun Obasanjo.

Rahoton nan ya bi ya tattaro suna da gajeren bayanin duk wanda ya taba rike ICPC.

ICPC HQ
Ofishin Hukumar ICPC Hoto: ICPC Nigeria
Asali: Facebook

1. Mustapha Akanbi

Da aka kafa ICPC a 2020, tsohon shugaban kotun daukaka kara, Muhammad Mustapha Adebayo Akanbi ya fara rike ta har zuwa shekarar 2005.

Kara karanta wannan

Nyesom Wike Ya Kinkimo Doka, Marasa Biyan Haraji Za Su Tafi Kurkuku a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Emmanuel Ayyola

Daga nan kuma sai ragamar ta koma hannun Emmanuel Olayinka Ayoola wanda lauya ne da ya yi aikin alkalanci a Najeriya da kasar Sierra Leone.

3. Uriah Angulu

Farfesa Uriah Angulu bai dade a ofis ba sai gwamnatin Goodluck Jonathan ta yi waje da shi a shekarar 2011, har ya sauka ba a tabbatar da shi a kujerar ba.

4. Dr. Rose Abang-Wushishi

A shekarar ta 2011 sai da aka samu shugaba har uku a ICPC, Dr. Rose Abang-Wushishi ta na cikinsu, ta yi kusan watanni biyar ta na rike da mukamin.

5. Abdullahi Bako

Daga matsayin wakilin Arewa maso gabas ne Abdullahi Bako ya jagoranci ICPC a matsayin shugaban rikon kwarya daga Agusta zuwa Nuwamba a 2011.

6. Eko Una Owo Nta

Barista Eko Una Owo Nta ya shafe shekaru shida a matsayin shugabar ICPC, wa’adinta ya fara tun daga tsakiyar shekarar 2012 zuwa farkon 2018.

Kara karanta wannan

Sabon Shugaban EFCC Ya Shiga Ofis, Zai Tono Binciken Tsofaffin Gwamnoni 25

7. Bolaji Owasanoye

Bayan tafiyar Eko Owo Nta, sai aka dauko Farfesa Bolaji Owasanoye wanda ya shugabanci ICPC har sai da Bola Tinubu ya nada wani sabon shugaba.

8. Musa Aliyu

A watan Oktoban nan ne aka rahoto Cif Ajuri Ngelale ya na cewa shugaba Bola Tinubu ya zabi Dr. Musa Aliyu domin ya zama sabon shugaban ICPC.

Nadin mukaman Tinubu

Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta saba lashe aman da ta yi wajen nadin mukamai a an ji labarin yadda ta ke bada mukami sai kuma ta janye.

Matasa irinsu Maryam Shetty da Imam Kashim Imam sun ga samu da rashi a lokaci daya a sabuwar gwamnatin da aka kafa a Mayun 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng