Tinubu Ya Ce Gwamnati Za Ta Kaddamar da Shirin Ba da Lamunin Dalibai a Watan Janairun 2024
- Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa lamunin karatun dalibai zai fara aiki a farkon shekarar da za mu shiga ta 2024
- Tinubu ya bayyana haka ne a yau Litinin 23 ga watan Oktoba a Abuja yayin babban taron tattalin arziki na kasa
- Shugaban ya ce wannan shiri na ba lamuni ga dalibai zai taimaka wurin rage yawan yajin aiki a manyan makarantu
FCT, Abuja – Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana cewa lamunin dalibai da ya kirkiro zai fara aiki a watan Janairun shekarar 2024.
Tinubu ya ce ba da wannan lamuni zai kawo karshen yajin aiki da ake yawan yi a manyan makarantun kasar baki daya, Legit ta tattaro.
Meye Tinubu ya ce kan lamunnin dalibai?
Shugaban ya bayyana haka ne a yau Litinin 23 ga watan Oktoba a Abuja yayin taron Tattalin Arziki na Kasa (NESG) karo na 29.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
TheCable ta tattaro cewa Tinubu ya kirkiro shirin ne na ba da lamuni ga dalibai musamman ga marasa karfi don samun damar yin karatu.
Tinubu ya bayyana himmatuwar gwamnatinsa na kawo sauyi musamman a tattalin arzikin kasar.
Ya bukaci hadin kan dukkan ma su ruwa da tsaki don tabbatar da samun wani tsari da zai dakile cin hanci da rashawa a kasar.
Wane albishir Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya?
Ya ce:
"Zuwa watan Janairun 2024, za mu fara shirin lamunin dalibai don inganta rayuwar 'ya'yanmu.
"Hakan zai kawo karshen yajin aiki da ake yawan yi a manyan makarantun kasar."
Shugaban ya ce 'yan Najeriya su na shan wahala na cire tallafin man fetur amma ya ce wannan na dan lokaci kada ne.
Ya kara da cewa tabbas nan gaba kadan za su ji dadin wannan mataki da ya dauka na cire tallafin mai a kasar.
Bashin Karatu: Kamata Ya Yi Dalibai Su Yi Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Tsarin, In Ji Mai Fashin Baki
Tinubu ya rattaba hannu kan shirin ba da lamunin dalibai
A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya amince da kuma rattaba hannu a tsarin bai wa dalibai lamunin karatu.
Tinubu yayin rattaba hannun ya ce hakan zai bai wa dalibai musamman marasa karfi daman yin karatu.
Dalibai da dama na murna ganin yadda su ke sa tsammanin shirin zai taimaka musu wurin inganta karatunsu.
Asali: Legit.ng