"Babban Kuskuren Da Tinubu Yake Tafkawa Wajen Haddasa Tashin Dala a Kasuwa", Dakta Bello
- Har yanzu an gagara tsaida darajar Dala da sauran kudin kasashen waje a wuri daya, watanni bayan an yi canjin gwamnati
- Masanin tattalin arziki, Dr. Usman Bello ya fada mana idan kasa ta karya darajar kudinta, za a fi sayen kayanta a kasashen waje
- A cewarsa, babu hikima a tsarin da ake kai domin Najeriya ta na sayo ne daga waje, karya Naira sai dai ya jawo karin talauci
Abuja - Naira ta na cigaba da karyewa a kan Dala a kasuwar canji, yanzu haka farashin kudin Amurka ya doshi N1, 200 a Najeriya.
Rahotanni sun ce a karshen makon jiya, an saida Dalar Amurkan ne tsakanin 1,175/$ da 1,190/$ a sakamakon karancin kudin wajen.
A kafar I & E da ake warewa ‘yan kasuwan kasa-da-kasa, Naira ta yi hobbasa kadan zuwa 808.28/$ a ranar Juma’a daga 810.05/$.
Ra'ayin masani a kan faduwar Naira
A hirar mu da Dr. Usman Bello, masanin tattalin arziki a jami’ar ABU Zariya, ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta na babban kuskure.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin jami’ar ya ce cire tallafi a kan kudin kasashen waje da aka yi a mulkin nan, shi ya ke jawo farashin Dala ya na yawo a kasuwa.
"A duniya babu kasar da za ta ce ba ta fitar da kayanta zuwa kasashen waje kuma ta bar darajar kudinta ya na yawo haka nan.
Ba a yin haka, ga kasar da ta ke saida kaya a ketare, idan ta karya darajar kudinta, za a fi sayen kayan da ta ke samarwa."
- Dr. Usman Bello
Inda Tinubu ya yi kuskure
Masanin ya ce kuskure ne CBN ya karya Naira alhali Najeriya ba ta iya samar da kaya ta kai wasu kasashe, hakan zai kara haifar da talauci.
Akwai nau’o’in kula da kudin kasashen waje iri-iri, abin da ake yi yanzu a Najeriya shi ne an bar farashi ya na yawo a hannun ‘yan kasuwa.
A ra’ayinsa akwai rashin hikima a kan yadda aka bar masu asusun kudin waje su ka karu, hakan zai kara azalzala faduwar da Naira ta ke yi.
Tsarin bankin CBN ya fara aiki?
Kwanaki bayan halatta bada kudin ketare domin shigo da kayayyaki 43 wanda a baya CBN ya hana, Naira na ta tangal-tangal a kasuwa.
Shugaban kungiyar ‘yan canji, Dr. Aminu Gwadabe ya ce idan ana so Naira ta farfado, dole sai an hada-kai da su da ke sarin kudin kasashe.
Asali: Legit.ng