UNICEF Na Fargabar Isra’ila Za Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Jarirai a Gaza
- Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana kokenta kan halin da jarirai za su shiga a Zirin Gaza sakamakon farmakin Isra'ila
- Isra'ila na ci gaba da kai farmaki kan al'ummar Falasdinu tun bayan da Hamas ta kai musu farmaki a ranar 7 ga watan Oktoba
- Ya zuwa yanzu, an kashe yara, mata, da tsofaffi da gama garin jama'a a yankin Gaza dama da 4300 inji hukumomin Hamas
Hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi a ranar Lahadi cewa rayukan akalla jarirai 120 da aka haifa a asibitocin Gaza ne ke cikin hadari yayin da aka toshe hanyoyin shigar man fetur yankin, rahoton Channels Tv.
Hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi a ranar Lahadi cewa rayukan akalla jarirai 120 da aka haifa a asibitocin Gaza ne ke cikin hadari yayin da aka toshe hanyoyin shigar man fetur yankin.
Halin da asibitocin Gaza ke ciki a yanzu
Asibitoci na fuskantar matsanancin rashin magunguna, man fetur da ruwa ba wai ga dubban da suka jikkata a makwanni biyu na kisan Isra'ila ke ci gaba da yi ba, har ma da marasa lafiya na yau da kullum.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar kakakin UNICEF, Jonathan Crickx:
"A halin yanzu muna da jarirai 120 da ke cikin kwalba, daga cikinsu muna da jarirai 70 da ke kan iskar gas, kuma ba shakka nan ne muka damu matuka."
Babban abin da ake bukata
Wutar lantarki na daya daga cikin manyan bukatun asibitocin kwararrun bakwai na Gaza da ke kula da jariran bakwaini, Al-Jazeera ta ruwaito.
Haka nan, a nan ne aka daura jariran a injunan numfashi da ba da tallafi mai mahimmanci, duba da yadda jikinsu bai yi kwari ba.
Isra'ila dai ta ba da umarnin mamayewa da katange yankin baki daya bayan harin Hamas, inda tace sojojinta su kashe kowa; har da tsofaffi da jarirai a Zirin Gaza.
An kashe karin Falasdinawa 55 a Gaza
A bangare guda, wani kazamin farmakin cikin dare da sojin Isra'ila suka kai kan mutanen da basu ji ba basu gani ba a Zirin Gaza ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 55 a daren Lahadi.
A cewar hukumomin kasar, mutum 55 ne suka yi shahada a harin da sojin na Isra'ila ke ci gaba da kaiwa Falasdinawa tun rikicin da ya barke a ranar 7 ga watan Oktoba.
Hukumomin sun kuma bayyana cewa, Isra'ila ta rushe gidaje sama da 30 a cikin kankanin lokaci a farmakin da ya dauki sa'o'i kadan, Channels Tv ta ruwaito.
Asali: Legit.ng