Gwamnatin Kaduna Ta Rufe Makarantar Mahaifin Sheikh Makari a Zaria Kan Dukan Dalibi Har Lahira
- Gwamnatin Kaduna karkashin jagorancin Uba Sani ta rufe makarantar Al-azhar da ke Zaria
- Ana zargin wasu malaman makarantar sun yi wa wani dalibi duka har lahira saboda ya yifashin zuwa makaranta
- Mahaifin Sheikh Ibrahim Ahmad-Makari, babban limamin masallacin kasa ne ke da makarantar
Jihar Kaduna - Hukumar da ke kula da tabbatar da ingancin Makarantun Jihar Kaduna (KSSQAA), ta rufe makarantar Al-azhar da ke Zaria bisa zargin dukan wani daliba har lahira.
Makarantar mallakin mahaifin babban limamin masallacin kasa, Sheikh Ibrahim Ahmad-Makari ne, jaridar Daily Nigerian ta rahoto.
Dalilin rufe makarantar Al-azhar da ke Zaria
An rahoto cewa wasu malamai sun yi wa wani dalibin JSS 3 na makarantar mai suna Marwan Sambo, dan shekaru 19 mugun duka har lahira saboda ya yi fashin zuwa makaranta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata sanarwa da ya gabatarwa manema labarai a ranar Lahadi, 22 ga watan Oktoba a Kaduna, Dr Usman Abubakar, darakta Janar na hukumar KSSQAA, ya ce ma'aikatar ilimi na jihar, da ke wakiltan gwamnatin jihar da makarantar ta fara gudanar da bincike.
Ya ce ziyarar da suka kai Zaria don tattara bayanan abun da ya faru ne daga makarantar Al-Azhar Academy, inda abun ya faru, uwa gidan yaron, don mika ta'aziyya da tattaunawa da iyalan marigayin da wasu abokan karatunsa.
Mista Abubakar ya kara da cewar tawagar hukumar KSSQAA sun ziyarci hedkwatar yan sanda da ke Zaria, inda ana tsare shugaba da mataimakin shugaban makarantar, rahoton The Cable.
Ya ce:
"Daga nan sai tawagar gano gaskiya suka garzaya babban asibitin Hajiya Gambo Sawaba, Zaria, inda aka tabbatar da mutuwar yaron.
"Daga karshe, tawagar KSSQAA ta ziyarci makabarta inda aka binne margayin, sannan an dudduba sabon kabarin.".
Za mu yi bincike da tabbatar da adalci, hukumar KSSQAA
Saboda haka, darakta janar din ya bayyana cewa gwamnatin jihar karkashin jagorancin Uba Sani, ya ba jama'a tabbacin cewa hukumarsa za ta tabbatar da samar da yanayin koyon karatu mai kyau, daidaito da adalci.
Ya kuma bukaci jama'a da su ci gaba da kwantar da hankalinsu da bin doka yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don yin adalci.
Ya ce:
"A san lokacin, bisa tsarin tanadin dokarta na 2015, hukumar KSSQAA ta rufe makarantar Al-Azhar Academy, Zaria kuma harabar makarantar zai ci gaba da kasance a kulle zuwa lokacin da sakamakon binciken zai fito."
An kama shugaba da mataimakin shugaban makaranta a Zaria kan kisan dalibi
A baya mun ji cewa yan sanda sun kama shugaba da mataimakin shugaban makarantar Al-Azhar da ke Zaria, jihar Kaduna kan zargin dukan dalibin JSS3, Marwanu Nuhu Sambo har lahira.
An yi zargin cewa wadanda ake zargin sun hadu sun yi wa Sambo hukunci mai tsanani wanda ya yi sanadiyar mutuwarsa a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba, rahoton The Nation.
Asali: Legit.ng