Kwantena Ta Fado Daga Bayan Tirela, Ta Murkushe Wata Mata Har Lahira a Anambra
- Wata mata da har yanzu ba a gano bayananta ba ta rasa rayuwarta yayin da wata kwantena ta faɗo daga bayan Tirela a jihar Anambra
- Kwantenar mai tsawon kafa 40 ta murkushe matar har lahira a yankin Ize-Iweka da ke garin Onitsha ranar Alhamis
- Kwamandan hukumar FRSC reshen jihar ya jajanta wa iyalan matar kana ya gargaɗi masu ababen hawa su bi doka
Jihar Anambra - Tsautsayi baya wuce ranarsa, wata Kwantena mai tsawon ƙafa 40 ta murkushe wata mata da ba a gama tantance wacece ba har lahira a jihar Anambara.
Babbar Kwantenar ta kutto ne daga kan Tirela a garin Onitsha, ta danne matar ba zato ba tsammani kuma lamarin ya zo da ƙarar kwana, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a unguwar Eze-Iweka da ke da yawan jama’a kusa da tashar motocin Upper Iweka kan titin Onitsha zuwa Owerri, a garin Onitsha.
Yadda kwamtenar ta danne matar
Ganau sun ce lamarin ya faru ne lokacin da da Tirelar, wadda ke tsaye a gefen titi ana sauke kaya, ta kutto ba tare da direba na ciki ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa, a yayin da hakan ta faru ne kwantenar mai tsawon ƙafa 40 da take dauke da ita ta faɗo ta murkushe matar da ke tsaye a bakin hanya.
Wata majiya ta ce Allah ne ya kiyaye da mutane sun mutu domin yayin da masu Tireda suka hangi motar na mirginowa, nan take suka yi gaggawar yin takansu.
Wane mataki mahukunta suka ɗauka?
Muƙaddashin kakakin hukumar kiyaye haɗurra reshen jihar Anambra, Margaret Onabe, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce tsautsayin ya faru ne da ƙarfe 3:00 na yamma.
Onabe ta alakanta musabbabin hadarin da lalacewar birki, inda ta kara da cewa tawagar ‘yan sandan ta yi kokari tare da nemo janwe ta ɗauke kwantenar mai tsayi.
"Jami'an ceto na FRSC da 'yan sanda sun garzaya wurin kuma sun yi kokarin nemo motar ɗaukar kaya domin janye kwantenar daga kan matar," in ji ta.
Ta kara da cewa kwamandan FRSC na jihar, Adeoye Irelewuyi, ya jajanta wa iyalan matar tare da gargadin masu ababen hawa kan bijirewa dokokin hanya, Guardian ta ruwaito.
Yadda Aka Yi Jana'izar Ambasadan Najeriya Na Morocco
A wani rahoton kuma Daga ƙarshe, an yi wa marigayi Magajin garin Zazzau Sallar jana'iza kuma an kai shi makwancinsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Gwamnan Kaduna, Uba Sani, Malam Nasiru El-Rufai da shugaban majalisar wakilan tarayya sun halarci jana'izar a Zariya.
Asali: Legit.ng