Abun Farin Ciki Yayin da Tinubu Ya Amince Da Kafa Sabbin Jami’o’i 7
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da mayar da manyan kwalejojin ilimi guda hudu zuwa jami’o’in ilimi ta tarayya
- Tinubu ya kuma amince da kafa sabbin manyan makarantun jami'o'i guda bakwai a fadin kasar
- Shugaban kasar ya kuma amince da sauya kwalejojin ilimi guda biyu zuwa jami’o’in ilimi na tarayya
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa wasu sabbin jami'o'in tarayya guda bakwai a fadin kasar.
Mataimakin daraktan labarai da hulda da jama'a, Obilor-Duru Augustina Okechi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a madadin ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba.
Kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta rahoto, Tinubu ya amince da kafa jami'o'in noma na tarayya guda biyu, jami'o'in likitanci da kiwon lafiya na tarayya biyu da kuma kwalejojin ilimi biyar.
Shugaban kasar ya kuma amince da mayar da manyan kwalejojin ilimi guda hudu zuwa jami’o’in ilimi na tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Okechi ya ce hakan ya yi daidai da kudurin Tinubu na tabbatar da ci gaba wajen gudanar da mulki da kuma daidaitan manufofi, rahoton Daily Trust.
“Kafawa da kuma canza wadannan makarantu yana kara nuna ajandar Shugaba Tinubu a bangaren ilimi kuma zai taimaka wajen inganta damar samun ilimin makarantun gaba da sakandare a kasar.”
Okechi ya bayyana cewa za a fara kafa wadannan makarantu da aka amince da su nan take a wadannan makarantu:
- Jami'ar Tarayya na likitanci da Kimiyyar Lafiya, Kwale, Jihar Delta
- Jami'ar noma ta tarayya, Mubi, jihar Adamawa
Kwalejojin Ilimi da suka koma Jami'o'in Ilimi na Tarayya
- Kwalejin ilimi na Adeyemi, Ondo, jihar Ondo
- Kwalejin ilimi tara tarayya na Alvan Ikoku, Owerri, jihar Imo
Kwalejojin ilimi
- Kwalejin ilimi ta tarayya, Ilawe Ekiti, jihar Ekiti
- Kwalejin ilimi ta tarayya, Ididep, Ibiono, jihar Akwa Ibom
- Kwalejin ilimi ta tarayya, Yauri, jihar Kebbi
Tinubu ya nada Shaakaa Chira a matsayin sabon mai binciken kudi na kasa
A wani labarin, mun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya zabi Mista Shaakaa Chira a matsayin sabon babban mai binciken kudi na kasa (AGF).
Wannan nadin ya biyo bayan nasarar tantance Mista Chira da hukumar kula da ma’aikatan gwamnatin tarayya (FCSC) ta yi, inda ta ayyana shi a matsayin wanda ya fi cancanta.
Asali: Legit.ng