Mutane Sun Yi Takansu Yayin da Yan Fashi Suka Kutsa Kai Cikin Bankuna a Benue
- Wasu 'yan fashi da makami sun kai hari kan bankuna biyu a garin Otukpo da ke jihar Benuwai da yammacin yau Jumu'a, 20 ga watan Oktoba
- An tattaro cewa mutanen garin sun yi takansu yayin da maharan suka shiga da misalin karfe 3:30 kuma sama da wa ɗaya suna cin karensu babu babbaka
- Wani mazaunin garin ya ce an kashe 'yan banga biyu a musayar wuta, har yanzu hukumar 'yan sanda ba ta ce komai ba
Jihar Benue - Mazauna garin Otukpo a jihar Benuwai sun yi takansu ranar Jumu'a yayin da wasu 'yan fashi da makami suka shiga bankuna biyu a tsakiyar garin.
Ganau sun bayyana cewa 'yan fashin sun farmaki bankunan biyu da misalin ƙarfe 3:30 na yammaci inda suka ci karensu babu babbaka har kusan ƙarfe 4:50.
Wani mazaunin garin wanda ya roƙi a sakaya sunansa ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa mutane sun ari da kare domin tsira da rayuwarsu bayan maharan sun shigo.
A ruwayar shafin Linda Ikeji, Mutumin ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Sun shiga bankin First Bank da Zenith Bank sun yi fashi ɗaya bayan ɗaya. Sun kutsa kai cikin bankunan da misalin ƙarfe 3:30 na yamma."
"Yan banga biyu sun rasa rayukansu a yanzu haka da muke magana. Sai ruwan harsasai ake yi ta ko'ina kuma idan kun saurara a hankali, za ku ji sautin ƙarar harbe-harbe."
"Wurin da aka kai wannan hari yana kallon-kallo da caji ofos ɗin 'yan sanda kuma wannan ne karon farko da irin haka ta faru."
Hukumar 'yan sanda ta tabbatar
Jami’ar hulda da jama’a ta hukumar ‘yan sanda (PPRO) reshen jihar Benuwai, SP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta ce har yanzu ba ta samu cikakken bayani ba.
“Ban samu damar yin magana da DPO ko daya daga cikin jami’an da ke yankin ba amma na samu labarin kai harin. Ba na son in dame su don haka mu ba su wani lokaci."
Yan bindiga sun kai sabon hari a jihar Kwara
A wani rahoton kuma 'Yan bindiga sun kai hari garin Ora da ke yankin ƙaramar hukumar Ekiti ta jihar Kwara, sun yi garkuwa da mutane da dama.
Yayin wannan harin, an ce maharan sun shiga fadar basaraken yankin, Oba C.O Odeyemi, sun tafka ɓarna kuma sun kwashi kaya.
Asali: Legit.ng