Kotu Ta Raba Auren da Ya Shafe Shekara 9 Kan Buƙatar Matar a Kwara
- Ƙotu ta raba auren shekaru tara tsakanin Balkisu Imam da Nasir Imam kan buƙatar da matar ta nema a jihar Kwara
- Alkalin Kotun ya kuma damƙa amanar kula da ɗan da suka haifa ɗan shekara 8 a hannun matar, kuma mijin ya riƙa daukar nauyinsa
- Tun farko, matar ta nemi saki a Kotun ne saboda abin da ta kira rashin kula da soyayya a zaman auren
Jihar Kwara - Wata kotun yanki da ke zama a Anguwar Centre-Igboro, Ilorin, babban birnin Kwara ta raba auren da ke tsakanin Balkis Imam da Nasir Imam.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Kotun ta datse igiyoyin auren da ke tsakanin Miji da matarsa, wanda aka ɗaura bisa tsarin Musulunci bayan shekaru tara suna tare.
Alkalin kotun, Mai shari'a Shehu Ajimobi ya amince da bukatar rabuwar ma'auratan wanda matar ta shigar tana neman a raba tsakaninta da mijinta.
Ajimobi ya umurci matar ta fara idda ta wata uku kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, sannan ya ba ta rikon yaronsu dan shekara 8.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma bai wa wanda ake kara damar zuwa ya ga ɗansu ba tare da takura ba amma a lokacin da ya dace.
Alkalin ya ce ya ɗauki wannan matakin ne saboda mijin ba shi da takamaiman aiki yi amma har yanzu yana son daukar nauyin ɗansa, kuma ba ya son rabuwa da matarsa.
Ya kuma umarci mijin ya ɗauki nauyin biyan kuɗin makarantar ɗan da suka haifa, kula da lafiyarsa da kuma walwala, Tribune ta ruwaito.
Meyasa matar ta nemi saki?
Tun a farkon shari'ar, Balkisu Imam ta shigar ƙarar tana mai neman a raba auren saboda abin da ta kira rashin nuna soyayya daga mijinta a zaman ibadar da take.
Ta kuma buƙaci a ba ta damar ci gaba da kula da ɗan da suka haifa guda ɗaya kuma a umarci tsohon mijin ya riƙa biyanta N10,000 duk wata na ciyarwa.
Kotu Ta Daure Wani Mutum Kan Kulla Auren Bogi
A wani rahoton na daban kuma Kotu ta garkame wani magidanci mai suna Gambo Adamu sakamakon damfarar surukarsa da kulla aure tsakaninta da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Harma ya kawo mata sadakinta N100,000 da wasu kyaututtuka da ya ce Buhari ne ya aiko da su bayan an daura masu aure.
Asali: Legit.ng