“Ka Tsayar Da Kiyayyar”: Reno Omokri Ya Wayar Da Kan Sheikh Gumi Bayan Ya Kira Wike “Shaidani”
- Wani mai sharhi kan harkokin zamantakewa, Reno Omokri, ya tsoma baki kan bayyana Nyesom Wike da Sheikh Gumi ya yi a matsayin shaidanin mutum
- Omokri wanda ya kadu da jin furucin Gumi ya bukaci yan Najeriya da su wanzar da soyayya sannan su kauracewa kiyayya
- Ya kuma bayyana cewa tushenmu daya gaba daya kuma babu addini a lahira illa soyayya
FCT, Abuja - Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya yi martani ga furucin da fitaccen malamin Musulunci Sheikh Ahmad Gumi ya yi.
Ku tuna cewa Gumi ya bayyana ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike a matsayin shaidanin mutum.
Gumi ya yi furucin ne yayin da yake watsi da tarban ambasan Isra'ila a Najeriya da Wike ya yi a ofishinsa da kuma shirin hada kai da Isra'ila kan lamarin tsaro a Abuja.
Da yake martani kan ci gaban, Omokri a wasu rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, 19 ga watan Oktoba, ya bayyana furucin Gumi game da rashin yarda da mika tsaron Najeriya a hannun kirista a matsayin "abun takaici da damuwa".
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Omokri ya kuma jaddada cewa irin wannan tunani na Gumi "ba shi da tushe”.
Jigon na jam'iyyar PDP ya tambayi Gumi ko ya fuskanci rashin tsaro a karkashin gwamnatin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai.
Sai dai kuma, ya bukaci yan Najeriya da su guji nuna kabilanci, su daina nunawa mutane kiyayya saboda addininsu sannan su mutunta addinin juna.
Ya ce:
“Maganar da Sheikh Gumi ya yi na rashin yarda da tsaron Najeriya a hannun kiristoci abin bakin ciki ne da damuwa. Mun kasance tare a matsayin kasa tsawon shekaru 63, kuma irin wannan maganar tana mayar da mu baya da kuma haifar da rashin yarda. Muna bukatar kwarewa da kishin kasa don magance matsalar rashin tsaro, ba addinin son zuciya ba. Shin Sheikh Gumi ya fuskanci irin rashin tsaro da ya gani a Kaduna a lokacin mulkin Nasir El-Rufai a lokacin gwamnatin Patrick Yakowa, Kirista? Wannan, tun a chan, karyata ra'ayinsa."
Omokri ya kara da cewar:
"Abin da ya kamata Sheikh Gumi ya fahimta shi ne, idan aka raba tagwaye a lokacin haihuwa, sannan ahlin Kirista da Musulmi suka karbi rikonsu, to za su girma kuma awkai yiwuwar za su dauki addinin iyayensu. Wannan ne yasa dole ne mu daina kyamar mutane a kan addininsu. Akasari ba su suke zabar addininsu ba. Shi ke zabarsu."
Shehu Sani ya yi martani bayan Sheikh Gumi ya kira Wike da “shaidanin mutum”
A wani labari makamancin wannan, tsohon dan majalisar tarayya, Sanata Shehu Sani ya nuna rashin jin dadinsa game da furucin Sheikh Ahmad Gumi a kan Nyesom Wike.
Sani ya ce ana iya sukar Wike a matsayinsa na wanda ke rike da mukamin gwamnati amma ba wai kan addininsa ba.
Asali: Legit.ng