'Rage Dogaro da Man Fetur Ne Kadai Hanyar Shawo Kan Matsalar Cire Tallafi', Sunusi Lamido

'Rage Dogaro da Man Fetur Ne Kadai Hanyar Shawo Kan Matsalar Cire Tallafi', Sunusi Lamido

  • Tsohon gwamnan CBN, Sunusi Lamido Sunusi ya bayyana hanyoyin da za a bi don kaucewa wahalalun cire tallafin mai a Najeriya
  • Tsohon Sarkin Kanon ya ce hanya mafi fa’ida kawai ita ce rage dogaro da man fetur a kasar tare da samo wata hanya daban
  • Sunusi ya bayyana haka ne a jiya Alhamis 19 ga watan Oktoba a jihar Legas lokacin da ya ke gabatar da wata lakca yayin wani taro

FCT, Abuja – Tsohon Sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi ya ce rage dogaro da man fetur ita ce kadai hanyar magance matsalar cire tallafin mai.

Sunusi ya bayyana haka ne a jiya Alhamis 19 a watan Oktoba yayin gabatar da lakca a jihar Legas,cewar TheCable.

Sunusi Lamido ya yi bayanin yadda za a shawo kan matsalar cire tallafi
Sunusi Lamido ya yi martani kan wahalhalun cire tallafi a Najeriya. Hoto: @hrhsanusi.
Asali: Facebook

Meye Sunusi ya ce kan cire tallafin mai?

Tsohon Sarkin ya ce ‘yan Najeriya sun dade su na maganan cire tallafi tun shekakar 2011 lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan.

Kara karanta wannan

Bashin Karatu: Kamata Ya Yi Dalibai Su Yi Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Tsarin, In Ji Mai Fashin Baki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce arzikin mai kadai bai isa ya mayar da kasar mai arziki ba amma kuma ya kai ya shigar da mu cikin matsaloli a Najeriya.

Ya ce:

“Mun fada idan ba mu yi wani abu ba kan wannan cire tallafin, za mu kara dawo wa inda mu ke ne a yanzu.
“Babban abin da zai shawo kan wannan matsalar ta cire tallafi shi ne rage dogaro da man fetur a kasar.
“Masana tattalin arziki sun ce Najeriya ba za ta taba zama mai arziki ba kawai don samar da mai da ta ke musamman idan aka kwatanta da Saudiyya.”

Wane gargadi Sunusi ya bayar kan sauraran masana?

Tsohon gwamnan CBN ya ce Saudiyya na fitar da gangan mai 91 ga kowa ne mutum daya a shekara yayin da Najeriya ke fitar da ganga 2.3.

Kara karanta wannan

Shetty, El-Rufai da Sauran Mutum 5 da Tinubu Ya Ba Mukamai, Sai Ya Dawo Ya Karbe

Ya kara da cewa kasar Kuwait na cire ganga 221 yayin da kasar Gabon da ke Nahiyar Afirka ke cire ganga 31.7.

Sunusi ya ce gwamnatin ba ta shirya kawo gyara ba tun da ba ta sauraran masana tattalin arziki inda ya ce babu yadda za a yi kullum ana abu daya a yi tsammanin sakamako daban, cewar Premium Times.

'Yan Najeriya su ka ba da kofa aka rena su', Sunusi Lamido

A wani labarin, tsohon Sarkin Kano, Sunusi Lamido ya bayyana cewa 'yan kasar ne su ka rena kansu a wurin 'yan siyasa.

Ya ce dole a rinka binciken 'yan siyasa idan ba haka ba, nan gaba babu wanda zai kira Najeriya kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.