Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Kebbi da Wasu 12
- 'Yan bindiga sun tare wata motar haya, sun sace tsohon shugaban ƙaramar hukuma da wasu mutane 12 a jihar Kebbi
- Rahotanni sun nuna cewa maharan sun tare motar, wacce ta taso daga Abuja a kan titin Tegina zuwa Kontagora
- Gwamnatin jihar Kebbi karƙashin Ƙauran Gwandu ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce zasu yi kokarin ceto su cikin ƙoshin lafiya
Jihar Kebbi - Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon shugaban karamar hukumar Ngeski a jihar Kebbi, Garba Hassan, tare da wasu mutane 12 a jihar Neja.
Hassan da sauran fasinjojin da ke cikin motar haya na kan titin Tegina zuwa Kontagora a jihar Neja da tsakar ranar Alhamis lokacin da aka sace su, This Day ta ruwaito.
An ce dukkan wadanda abin ya shafa na kan hanyarsu ta zuwa Kebbi ne daga Abuja a cikin motar haya lokacin da lamarin ya afku, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Yan bindigar sun yi ta laɓewa a cikin dajin da ke tsakanin Tegina da garin Kontagora a Jihar Neja, inda suka far wa hanyar tare da tsayar da motar da Hassan da sauran su ke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun bayyana cewa bayan tare motar, 'yan bindiga suka tasa ƙeyar mutanen daga wurin zuwa cikin daji kuma har yanzun ba a san inda suka kai su ba.
Wane mataki mahukunta suka ɗauka kan lamarin?
Sakataren watsa labaran gwamna Nasir Idris (Ƙauran Gwandu), Ahmed Idris, ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho, kamar yadda Dailypost ta ruwaito.
"Mun ji labarin abin da ya auku, muna kan binciken lamarin da ya kai ga garkuwa da shi," in ji Idris, ya kara da cewa "za a yi komai don ganin an sako Alhaji Garba Hassan."
Amma da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya ce, “zan yi bincike na tattara bayanai sannan sai na dawo gare ku."
Jakadan Najeriya Kuma Ɗan Uwan Mai Martaba Sarkin Zazzau Ya Rasu
A wani rahoton kuma Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya yi wa jakadan Najeriya a Morocco, Alhaji Mansur Nuhu Bamalli, rasuwa.
Marigayin shi ne Magajin Garin Zazzau kuma ƙanin mai martaba Sarkin Zazzau, ya rasu ne a asibitin Kudi a jihar Legas.
Asali: Legit.ng