Shetty, El-Rufai da Sauran Mutanen da Tinubu Ya Ba Mukami, Ya Dawo Ya Karbe

Shetty, El-Rufai da Sauran Mutanen da Tinubu Ya Ba Mukami, Ya Dawo Ya Karbe

  • Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya na cigaba da rabon mukamai a gwamnatinsa, amma a wani lokacin ya na yin tafka da warwara
  • Sai shugaban ya sanar da nadin mukami, sai kwatsam ya fitar da wata sanarwa ta dabam, ana janye mukamin da aka yi niyyar yi
  • Maryam Shetty ta ga samu da rashi lokaci daya a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da aka yi mata bukulun zama ministar tarayya

AbujaNade-naden mukaman da Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ke yi su kan jawo surutu, wani lokacin har ta kai a warware su.

Nadin shugaban hukumar EFCC ya na cikin wadanda aka yi ta maganganu a kai, har ana zargin fadar shugaban kasa ta saba tsarin mulki.

A rahoton nan, abin da mu ka kawo shi ne sunayen duk wadanda irin haka ta faru da su a cikin watanni kusan biyar da canjin gwamnati:

Kara karanta wannan

Za Su Kashe Ni – Abokin Fadan Kwankwaso a NNPP Ya Ce Ya Na Fuskantar Barazana

Bola Ahmed Tinubu
Imam Kashim Imam da Maryam Shetty Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

1. Imam Kashim Imam

Kafin ayi mako daya da nada Ibrahim Kashim Imam, sai ga sanarwa daga fadar shugaban kasa inda aka sanar da soke nadin ‘dan shekara 24 din.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Maryam Shetty

A lokacin da Bola Tinubu ya zabi Maryam Shetty a cikin Ministocinsa, hakan ya tada kura har APC, daga baya sai ya maye gurbinta da wata dabam.

3. Nasir El-Rufai

An zabi Nasir El-Rufai kuma an tantance shi domin ya sake zama Minista a majalisa, sai aka ji an yi waje da tsohon Gwamnan da sunan dalilin tsaro.

4. Stella Okotete

Stella Oketete ta na cikin wadanda ba su da rabon zama Ministocin Tinubu, majalisar dattawa ba ta amince da nadin tsohuwar shugabar ta FRSC ba.

5. Abubakar Danladi

Na karshe shi ne Sanata Abubakar Danladi wanda shi ma majalisar dattawa ta nuna ba ta yarda ya zama minista ba saboda dalilan da ta kira na tsaro.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fara Sabon Yunkuri Domin Hana Amurka Fallasa Ragowar Sirrinsa a Duniya

Nadin Imam Ibrahim Kashim

Ku na da labari an haifi Injiniya Imam Ibrahim Kashim ne a watan Disamba ta shekarar 1998 daf da Olusegun Obasanjo zai zama shugaban kasa.

Tun can jama’a sun yi ta suka ganin yadda aka dauki wanda bai dade da gama jami’a ba, aka bukaci ya kula da babbar hukuma a kasa irin FERMA.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng