Tsohon Minista Ya Tona Ainihin Wadanda Su ke Hana a Gyara Wutar Lantarkin Najeriya

Tsohon Minista Ya Tona Ainihin Wadanda Su ke Hana a Gyara Wutar Lantarkin Najeriya

  • Barth Nnaji ya san harkar wuta domin ya rike Ministan lantarki a lokacin da Goodluck Jonathan ya ke kujerar shugaban kasa
  • Tsohon Ministan ya nuna yadda ‘yan kasuwa su ke hana ruwa gudu, su ke bakin kokarinsu wajen ganin lantarki bai zauna ba
  • Farfesa Nnaji yake cewa masu shigo da dizil su na ganin idan kowa ya samu isasshen wuta, kasuwancinsu ya ruguje har abada

Abia - Barth Nnaji wanda ya yi Ministan harkokin wutar lantarki a kasar nan, ya yi bayani game da abin da ya ke kawo cikas har kullum.

A wata zantawa da aka yi da shi a gidan rediyon Flo FM da ke garin Umuahia a jihar Abia, Farfesa Barth Nnaji ya haska matsalar Najeriya.

Farfesan ya zargi manyan dillalan janareto da masu shigo da man dizil da kawo matsala wajen kokarin ganin an samar da isasshen wuta.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fara Sabon Yunkuri Domin Hana Amurka Fallasa Ragowar Sirrinsa a Duniya

Wutar Lantarkin Najeriya
Akwai matsalar wutar lantarki a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Lantarki ya zama kayan gabas

Barth Nnaji yake cewa daukewar da babbar tashar Najeriya ta ke yi matsala ce da aka gagaro kawo karshenta, kuma abin damuwa ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yanzu haka Nnaji shi ne shugaban kamfanin Geometric Power da ke garin Aba, ya ce masu janaerto da harkar dizil sun zama ala-ka-kai.

Abin da tsohon Minista ya fada

"Akwai bangarori biyu idan ana maganar masu hana ruwa gudu a bangaren nan – masu shigo da man dizil da kuma masu injinan janero.
Najeriya na cikin manyan inda ake amfani da janaretoci saboda matukar bukatar wutanmu, ‘yan kasuwa ba za su so daukewar wuta ba.
Masu shigo da dizil su na ganin cewa idan lantarki ya zauna, kasuwancinsu zai lalace."

- Barth Nnaji

P/Times ta rahoto shi ya na cewa an taba lalata wata na’urar wuta, da aka bincika sai aka gano masu dizil ne su ka sa aka yi danyen aikin.

Kara karanta wannan

Shetty, El-Rufai da Sauran Mutum 5 da Tinubu Ya Ba Mukamai, Sai Ya Dawo Ya Karbe

A cewarsa, ana bukatar kwararru wanda su ka san harkar lantarki su shiga sha’anin, ba a bar abin a hannun wadanda ba su lakance shi ba.

Ana kashe kudi kan lantarki a banza?

Ana ganin cewa duk da gwamnatin tarayya ta na ta kara kudi domin a samu wutar lantarki sosai, har yanzu maraba jiya da yau kadan ce.

Tun da Goodluck Jonathan ya cefanar da kamfanonin wuta a 2013, har yau ana gidan jiya. Ana ikirarin gwamnati ta kashe N7tr zuwa yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng