Gwamna Zulum Ya Ba Leburori 37 Tallafin Karatu a Jami'a a Jihar Borno
- Farfesa Babagana Umaru Zulum ya yi alƙawarin ɗaukar nauyin karatun ma'aikatan gini 37 a jihar Borno
- Yayin wata ziyarar duba aiki da ya je ranar Alhamis, Zulum ya gano ma'aikatan suna da shaidar kammala Sakandire
- Ya ce duk wanda ya samu gurbi a jami'a daga cikinsu, gwamnati zata ɗauki nauyin komai har ya gama karatu
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya yi alƙawarin ɗaukar nauyin leburori 37 su yi karatun digiri a jami'o'i.
Gwamna Zulum ya yi alƙawarin wannan tagomashin tallafin karatu ga Leburorin da ke aiki gina gidajen 'yan gudun hijira a ƙauyen Nguro Soye, ƙaramar hukumar Bama a jihar Borno.
Farfesa Zulum ya ɗauki wannan alƙawari ne yayin da ya kai ziyarar gane wa idonsa wurin aikin ginin ranar Alhamis, 19 ga watan Oktoba, 2023.
Hukumar dillancin labarai ta ƙasa NAN ta tattaro cewa yayin wannan ziyarar gwamna Zulum ya bada loƙaci ya tattauna da Leburorin da ke aiki a wurin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A tattaunawar ne gwamnan ya gano wasu daga cikinsu, mutum 37, suna da shaidar kammala karatun Sakandire (SSCE) amma ba su samu damar ci gaba da karatu ba.
Don haka ya ce duk wanda ya samu nasarar cin jarrabawar share fage har ya samu shiga kowace jami’a za a ɗauki nauyinsa baki ɗaya har ya gama karatunsa.
A sanarwan da ya wallafa a Facebook, Zulum ya ce:
"Ku sanar da ni adadin waɗanda suka kammala Sakandire daga cikin ku kuma zamu ɗauki nauyin ku, ku yi karatu a jami'a.
Gwamnan ya duba barnar Boko Haram a Kwaleji
NAN ta ruwaito cewa gwamnan ya kuma tantance gine-ginen da mayakan Boko Haram suka lalata a Kwalejin Ilimi, Kimiyya da Fasaha ta Umar Ibn Ibrahim (UIICEST), Bama.
Ya umurci kwamishinan sabunta gini, gyara da maida jama’a, Ibrahim Idriss, da ya zurfafa nazarin barnar da aka yi a rukunin gidajen ma’aikata da gidajen kwanan dalibai.
Ya yi nuni da cewa, gyara wuraren da aka lalata, zai ba ɗalibai da ma’aikata damar sake mamaye kwalejin wanda a halin yanzu ke aiki sama-sama.
Shugaban BOI Na Ƙasa Ya Yi Murabus Daga Kujerarsa, Bola Tinubu Ya Nada Sabo
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Dokta Olasupo Olusi a matsayin sabon shugaban bankin masana'antu na ƙasa BOI.
Kakakin shugaban kasa ya ce hakan ya biyo bayan murabus din da tsohon Manajan Daraktan BOI ya yi bisa ra'ayin kansa.
Asali: Legit.ng