“Ba Za a Yarda Da Haka Ba”: Shehu Sani Ya Yi Martani Yayin da Gumi Ya Kira Wike Da “Shaidanin Mutum”
- Sanata Shehu Sani ya yi martani ga furucin Sheikh Ahmad Gumi da ya bayyana Wike a matsayin "shaidanin mutum"
- Tsohon dan majalisar ya ce ana iya sukar Wike a matsayinsa na wanda ke rike da mukamin gwamnati amma ba wai ta fuskacin addininsa ba
- Sani ya ce kalaman da Gumi ya yi wa Wike a kan addininsa yana tattare da rashin tunani kuma ba za a amince da shi ba
FCT, Abuja - Tsohon sanata da ya wakilci Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa ana iya caccakar ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, a matsayinsa na wanda ke rike da mukamin gwamnati amma ba wai kan addininsa ba.
Sani ya ce yana adawa da amfani da "addini" a kan tsohon gwamnan na jihar Ribas don cimma son zuciya.
Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X @ShehuSani yayin da yake martani ga furucin da Sheikh Ahmad Gumi ya yi na cewa Wike shaidanin mutum ne kuma ya kamata a tsige shi a matsayin ministan Abuja.
"Ana iya sukar Wike kuma a soke shi a matsayin jami'in gwamnati amma yin amfani da sunan addini a kansa don cimma son zuciya rashin tunani ne kuma ba abun yarda ba."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin da zai sa Tinubu ya tsige Wike, Gumi
Da farko mun ji cewa fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, a matsayin shaidanin mutum kan tarban ambasadan Isra’ila a Najeriya a ofishinsa.
Malamin addinin ya bayyana hakan ne a wani bidiyo mai tsawon mintuna 14 da ya wallafa a shafinsa na Facebook, yayin da yake karantar da dalibansa.
A cikin wa'azinsa, Gumi ya kuma tabbatar da cewar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba zai yi mulki na shekaru takwas ba idan har bai tsige Wike daga matsayin ministan Abuja ba.
“Ba na adawa da addinin Musulunci a matsayin minista”, Wike ya magantu
A baya, Legi Hausa ta rahoto cewa ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya yi watsi da rahotannin da ke yawo cewa gwamnatinsa a Abuja na karfafa manufofin da suka sabawa addinin musulunci, jaridar The Nation ta rahoto.
Wike ya bayyana a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba, cewa masu ingiza ra’ayin addini suna yin hakan ne ta sigar yaudara domin samun karfi a siyasa.
Asali: Legit.ng