Tubabbun 'Yan Boko Haram 6,900 Ne Aka Sako Su Cikin Al'umma

Tubabbun 'Yan Boko Haram 6,900 Ne Aka Sako Su Cikin Al'umma

  • Akalla mayakan Boko Haram 6,900 aka sake su zuwa cikin al'umma bayan sun tabbatar da tubansu ga hukumomi
  • Mayakan kafin sakin nasu cikin al'umma an tantance su ciki da waje wanda daga bisani su ka shiga al'umma
  • Hadimin gwamnan jihar Borno a harkar tsaro, Janar Abdullahi Sabi shi ya bayyana haka yayin tantance tubabbun mayakan

Jihar Borno - 'Yan Boko Haram fiye da dubu 6 ne su ka dawo cikin al'umma bayan sun tuba daga aikata laifuka a jihar Borno.

Gwamnatin jihar ta sanar da cewa an gama tantance mayakan ne kafin barinsu dawo wa cikin al'umma don ci gaba da rayuwa.

Gwamnan Borno ya sako tubabbun mayakan Boko Haram dubu 6
Gwamnatin jihar Borno ta sako tubabbun mayakan Boko Haram. Hoto: Babagana Zulum.
Asali: Facebook

Meye gwamnatin Borno ke cewa kan tubabbun Boko Haram?

Hadimin gwamnan jihar a bangaren tsaro, Janar Abdullahi Sabi ne ya bayyana haka yayin tantance mayakan a Maiduguri babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mutane Sama da 35 Sun Mutu Yayin da Wasu Akalla 40 Suka Jikkata a Hatsari a Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aminiya ta tabbatar da cewa 'yan Boko Haram dubu 100 ne su ka tuba a radin kansu wanda daga ciki aka tantance 6,900 don dawo da su cikin al'umma bayan kawar da su kan akidarsu ta baya.

Janar Sabi ya ce an samu nasarar mayar da tubabbun 'yan Boko Haram din ne ga iyalansu bayan tantance su da hadin gwiwar jami'an tsaro da shugabannin addinai da sauransu, National Accord ta tattaro.

Wane korafi ake samu kan tubabbun Boko Haram?

Ya ce babu wani korafi da su ke samu daga jama'a a gari dangane da halayensu ko wani abu daban a tare da su.

Sai dai ya ce yabo kawai su ke samu daga jama'a inda aka sanar da su cewa tubabbun 'yan Boko Haram din da yawa sun yi aure wasu sun kama sana'o'i yayin da wasu su ka rungumi noma.

Kara karanta wannan

Kudin Asiri: Kotu Ta Yanke Wa Matasa 5 Hukuncin Shekaru 12 a Magarkama Kan Tono Kokon Kan Mutum

Ya kara da cewa kashi 85 na wadanda su ka mika wuyan ba a son ransu su ka shiga kungiyar ba tilasta musu aka yi.

Zulum ya ba da umarnin rushe gidajen karuwai

A wani labarin, Gwamna Babagana Zulum ya ba da umarnin rushe gidan karuwai da aikata badala a birnin Maiduguri na jihar.

Gwamna ZulumNe ya ba da wannan umarnin ne a ranar Talata 17 ga watan Oktoba a Maiduguri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel