Shehu Sani Ya Yi Martani Bayan Jam'iyyar LP Ta Bukaci Yan Majalisunta Ka da Su Karbi Motocin N160m
- Wata sanarwa da jam'iyyar Labour Party ta fitar a baya-bayan nan ga ƴan majalisarta, ya sanya mutane da yawa sun yi martani a shafukan sada zumunta
- Yayin da wasu da dama ke ganin cewa jam'iyyar na cigaba riƙo da akidar ta, wasu na ganin cewa hali ne kawai irin na siyasar Najeriya
- Tsohon sanata Shehu Sani ya bayyana umarnin jam’iyyar Labour a matsayin furucin kishin ƙasa, inda ya ce babu wani ɗan majalisa da zai mayar da motocin N160m
FCT, Abuja - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya mayar da martani bayan shugaban jam'iyyar Labour Party na ƙasa, Julius Abure, ya yi Allah-wadai da motocin N160m ƙirar SUV da za a ba kowane daga cikin ƴan majalisar wakilai 360.
Yayin da ya buƙaci ƴan majalisar jam'iyyarsa da su yi watsi da kyaututtukan, Abure ya bayyana matakin a matsayin ƙololuwar rashin hankali.
Da yake mayar da martani ta shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba, tsohon sanatan ya bayyana umarnin Abure a matsayin "kalami na kishin ƙasa".
Shehu Sani ya rubuta cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"LP ta gaya wa ƴan majalisunta na tarayya da su yi watsi da motocin da aka ware musu. Wannan magana ce ta kishin ƙasa. Sai dai babu wanda zai ƙi karɓar motocin."
Ƴan Najeriya sun mayar da martani kan kalaman Shehu Sani
ƴan Najeriya sun shiga sashen sharhi na shafin Shehu Sani na X inda suka bayyana ra'ayoyinsu kan matsayarsa.
Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin su.
@Onyeckerous ya rubuta:
"Akalla, jam'iyyar na ɗaukar matakin yaƙi da almubazzaranci da ɓarnatar da dukiya, bari mu ga ƴan majalisun da ke da dattakon da za su iya haɗiye kwaɗayinsu."
@ExquisiteDemola ta rubuta:
"LP yaudara ce kawai, jam'iyyar reshe ce ta PDP kuma suna da aƙidu da ƙa'idojin PDP."
@blessed_ajoke ta rubuta:
"Nagode da ka yarda cewa maganarta ta kishin ƙasa ce, amma mu jira mu ga ko za su karɓi motocin ko ba za su karɓa ba. Ka da ka yi saurin yanke hukunci."
@itsneme ta rubuta:
"A cikin wannan tattalin arziƙin na Najeriya? Ko wanda ya fitar da sanarwar ba zai yi watsi da N160m SUV ba. Dan Allah LP ku daina wasa."
@Ice_tweetz ya rubuta:
"Lol. Bana jin wani ɗan majalisa zai ƙi karɓar motar, babu wanda zai yi a cikinsu."
Majalisa Ta Ce a Bude Iyakoki
A wani labarin kuma, majalisar wakilai ta buƙaci gwamnatin tarayya ta wangale iyakokinta da Jamhuriyar Nijar.
Ƴan majalisun dai na son gwamnatin tarayya ta buɗe iyakokin ƙasar nan da Jamhuriyar Nijar na Ilela, Kongwalam, Maigatari da Mai'adua.
Asali: Legit.ng