Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon 'Rundunar' Tsaro Ta Jihar Katsina
A ranar 10 ga watan Oktoba, 2023, jihar Katsina ta buɗe wani sabon babi a ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin jihar da ke Arewa maso Yamma.
A wannan rana, gwamna Malam Dikko Radɗa ya jagoranci kaddamar da rundunar 'yan sa'kai Community Watch Corps domin kawo karshen 'yan bindiga a jihar.
A wannan shafi, za ku ji muhimman abubuwan da ya dace ku sani game da sabuwar rundunar tsaron da ta ja hankalin ɗaukacin 'yan Najeriya.
Kafa doka
Tun da farko, Gwamna Raɗɗa ya tura da kuɗirin kafa rundunar tsaron al'umma ga majalisar dokokin jihar Katsina, kuma ba ta jima ba ta amince sannan ya rattaɓa hannu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Katsina: Bayan Kafa Rundunar Tsaro, Gwamnatin Radɗa Ta Yi Magana Kan Yiwuwar Tattaunawa da 'Yan Bindiga
Duk wannan ya faru ne cikin mako biyu saboda amfanin da wannan dakarun 'yan sa'kai zasu yi a yaƙi da matsalar tsaron jihar wanda ya taɓa kananan hukumomi 22.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Katsina, Nasir Babangida Mu’azu, a wata hira ya ce jami'an tsaron suna da goyon bayan doka na aikin da zasu yi.
Horar da dakarun CWC
'Yan sa'kan sun ɗauki tsawon watanni biyu suna samun horo a tsanake daga kwararru ta yadda zasu shirya tsaf su tunkari babban aikin da ke gabansu.
Matasan da aka zakulo sun samu isasshen horo kan sarrafa makamai, yaki da ta'addanci, atisaye, bada agajin farko, dangatakar jami'in tsaro da fararen hula da sauran darussa.
Dakta Mu'azu ya ce rundunar na da ingantaccen tsari tare da kwamitin da ya kunshi wakilai daga dukkan hukumomin tsaro a matsayin waɗan da zasu ja gaba.
Kaddamar da rundunar 'yan sa'kai
Tabbas, 10 ga watan Oktoba, rana ce da zata jima a zukatan Katsinawa biyo bayan yaye rukunin farko na jami'an CWC 1,456, waɗan da za a tura kauyuka daban-daban.
Da yake jawabi a wurin, Gwamna Raɗɗa ya ce wannan na ɗaya daga cikin alƙawurran da ya ɗauka lokacin kamfe na bai wa sha'anin tsaro fifiko.
"Wannan bai kamata ya ba kowa mamaki ba duba da yadda 22 daga cikin kananan hukumomi 34 a Katsina suna fuskantar kalubalen tsaro sosai," in ji shi.
Makamai da sauran kayan aiki
Bayan kaddamar da su, Gwamnatin Katsina ta samar musu da motocin sulƙe 10, motocin sintiri kirar Toyota Hilux guda 70, babura 700 domin inganta ayyukansu.
Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da gwamnonin jihohin Jigawa, Kano, Zamfara, Kebbi, Sokoto, Yobe da sauran jiga-jigai ne suka halarci bikin a filin wasan Karkanda.
Katsinawa suna sa ran samun zaman lafiya
Tun bayan wannan lamari, mazauna Katsina sun nuna farin cikinsu da fatan alheri, kuma suna tsammanin wannan jami'ai zasu taka rawar gani.
Malam Auwal, ya shaida wa Legit Hausa cewa a halin yanzu ba bu abin da wannan gwamna da tawagar 'yan sa'kan nan su ke buƙata da ya fi addu'a.
Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Gidan Ɗan Majalisar Arewa, Sun Tafi da Matarsa da 'Ya'yansa
"Duk wani mai kishin Katsina ya ji daɗin wannan tsari na Radɗa, muna fatan mutane su ci gaba da yi musu addu'a, domin babu abinda ya gagari Allah, sannan mu gyara halayen mu."
A nasa bangaren, Sadik Abubakar, wani mazaunin Faskari, ya ce mazauna yankin na fatan za a samu raguwar matsalar tsaro sosai bayan kaddamar da jami’an tsaro na jiha.
Mafi akasarin mutanen da wakilin mu ya zanta da su kan wannan ci gaban sun bayyana sa ransu da samun sauki sanadin waɗan nan matasa da suka bada rayuwarsu.
"Ba Zamu Nemi Sulhu da Yan Bindiga Ba" Gwamnatin Katsina Ta Magantu
A wani rahoton kuma Gwamnatin Katsina ta tabbatar da cewa ba za ta tattauna da 'yan bindiga don neman sulhu ba.
Kwamishinan tsaro da harkokon cikin gida, Mu'azu Ɗanmusa ya jaddada kudirin gwamnatin Dikko na kawo karshen 'yan bindiga a jihar.
Asali: Legit.ng