Mutane Sama da 30 Sun Mutu a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Jihar Yobe

Mutane Sama da 30 Sun Mutu a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Jihar Yobe

  • Wani mummunan hatsarin mota ya yi ajalin mutane aƙalla 38, wasu kusan 50 na kwance a Asibiti a jihar Yobe
  • Ganau sun bayyana cewa wata Tirela maƙare da Shanu da mutane ce ta bugi motar kanta a hanyar zuwa Potiskum
  • Har kawo yanzu babu sanarwa a hukumance amma an ga jami'an agaji na kwashe mutane zuwa Asibiti

Jihar Yobe - Rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutane 38 suka mutu yayin da wasu sama da 40 ke kwance a asibiti suna jinya sakamakon wani haɗarin mota da ya auku a jihar Yobe.

Mummunan hatsarin ya auku ne a garin Potiskum da ke cikin jihar Yobe a Arewa maso Gabashin Najeriya ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba, 2023.

Hatsarin mota ya laƙume rayuka da yawa a jihar Yobe.
Mutane Sama da 30 Sun Mutu a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Jihar Yobe Hoto: Yobe State
Asali: UGC

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa wannan hatsari ya faru ne kan babban titin Nangere-Potiskum.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Majalisar Dattawa Ta Bi Umarnin Tinubu, Ta Tabbatar a Nadin Manyan Mukaman da Ya Tura

An tattaro cewa wata babbar Mota Tirela da ta ɗauko Shanu daga ƙauyen Buduwa da ke ƙaramar hukumar Jakusko da nufin zuwa Potiskum, ita ce ta yi karo da wata babbar motar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ganau ya bayyana cewa:

"Tirelar ta kutto a gudun da ya wuce ƙa'ida kuma ta kucce wa direban ta bugi wata babbar mota da ake kira da Kanta. Nan take ta halaka mutane 20, wasu 40 kuma suka ji raunuka."

Wata majiyar ta daban ta ce tirelar ta kuma murkushe wadanda suka fado daga babbar motar.

An ce mutanen da lamarin ya shafa suna kan hanyar zuwa babbar kasuwar nan ta shanu da ke garin Potiskum.

Har yanzu babu sanarwa a hukumance daga FRSC

Wani mai suna, Adamu Hassan, ya shaida wa Channels tv cewa a halin yanzun an ɗauke gawarwakin mutanen da suka mutu zuwa babban Asibitin Potiskum na musamman.

Kara karanta wannan

Katsina: Bayan Kafa Rundunar Tsaro, Gwamnatin Radɗa Ta Yi Magana Kan Yiwuwar Tattaunawa da 'Yan Bindiga

Sai dai har yanzun jami'an hukumar kiyaye haɗurra (FRSC) ba su tabbatar da faruwar haɗarin ba a hukumance.

Amma an ga jami'an hukumar bada agajin gaggawa suna ɗaukar waɗanda ya rutsa da su zuwa Asibiti.

'Yan Bindiga Sun Fasa Gidan Dan Majalisa, Sun Sace Matarsa da 'Yayansa

A wani rahoton kuma Yan bindiga sun yi garkuwa da mata ɗaya da 'ya'ya biyu na wani ɗan majalisar dokokin jihar Kwara da tsakar dare.

Rahoto ya nuna cewa maharan sun kutsa cikin gida, suka tafi da su da misalin ƙarfe 1:00 na dare kuma har yanzu ba a gansu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel