Ruwan Nadin Mukaman Tinubu Ya Shiga SON, An Nada Sabon Shugaba a Najeriya

Ruwan Nadin Mukaman Tinubu Ya Shiga SON, An Nada Sabon Shugaba a Najeriya

  • Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya cigaba da yin nade-naden mukamai a gwamnati, wannan karo ya shiga ma’aikatar kasuwanci
  • Dr. Ifeanyi Chukwunonso Okeke zai rike shugabancin Hukumar SON wanda ke da alhakin duba kyawu da ingancin kayayyaki a Najeriya
  • Kafin nan Shugaban kasa ya tsige shugabannin hukumomin CAC, ITF, NEPC, OGFZA, NSDC, ya nada masu sababbin shugabanni na kasa

Abuja - A kokarin ganin an gyara kyawun kaya a Najeriya, Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya nada wanda zai jagoranci hukumar SON.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa Ifeanyi Chukwunonso Okeke ya zama shugaban SON.

Sabon Darekta Janar din kwararren Akanta ne wanda yake da rajista da ICAN, ya yi digirinsa na farko, na biyu da na uku a ilmin Akantanci.

Shugaba a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu Hoto: @nosasemota
Asali: Twitter

Karatun Ifeanyi Chukwunonso Okeke

Baya ga digirin BSc, MSc da kuma PhD, Dr. Ifeanyi Chukwunonso Okeke ya na da shaidar digirgir na MBA a ilmin gudanar da kasuwanci.

Kara karanta wannan

"Yarbawa Kirista Ake Fifitawa": MURIC Ta Soke Tinubu Kan Nade-Nadensa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar da aka fitar ta ce kwararren Akantan ya yi karatu ne a jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke garin Awka da jami’ar Najeriya ta Nsukka.

Kwarewarsa ta hada da tattalin arziki, ilmin haraji da akantanci sannan shi ne tsohon shugaban hukumar tattara haraji na jihar Imo.

Dr. Ifeanyi Okeke zai kawo gyara a SON

Ana sa ran nadin da Tinubu ya yi zai taimaka wajen farfado da tattalin arziki ta hanyar bunkasa kanana da matsakaitan masana’antu.

Daga zuwansa SON, Dr. Okeke ya gabatar da manufofin da yake da su na kawo cigaba.

Burinsa shi ne nan gaba hukumar Najeriya ta zama jagora wajen tabbatar da ingancin kaya tare da kirkiro cigaba da kawo gyare-gyare.

Wannan ya na cikin namijin kokarin da gwamnatin Bola Tinubu mai-ci ta ke yi domin ganin an kawo gyara-gyara a karkashin jagorancinsa.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Soki Amurka a Kan Goyon Bayan Israila Wajen Hallaka ‘Yan Gaza

Tinubu ya yi kasafin N26tr a 2024

Rahoto ya zo cewa gwamnatin Najeriya ta tunanin yin kasafin da ba a taba ganin irinsa ba. Kasafi mafi tsada da aka yi shi ne N21tr a shekarar nan.

A shekarar farko a ofis, Bola Ahmed Tinubu ya na harin batar da abin da ya zarce N26tr. Daga cikin kudin, akalla 30% za su tafi wajen biyan bashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng