Dalibar Jami’a Ta Sheke Kanta Bayan Ta Rantawa Saurayin Da Suka Hadu a Intanet N500,000

Dalibar Jami’a Ta Sheke Kanta Bayan Ta Rantawa Saurayin Da Suka Hadu a Intanet N500,000

  • Wani abun bakin ciki ya riski al'ummar jami'ar Ilorin da ke jihar Kwara bayan mutuwar daya daga cikin dalibanta
  • Wata daliba mai shekaru 20, Sanni Hameedat, ta sheke kanta bayan saurayi ya damfareta kudi N500,000
  • Hukumar jami'ar ta ce dalibar ta sha maganin kashe kwari ne sakamakon matsin lambar da take fuskanta kan abun da ta aikata

Jihar Kwara - Rahotanni sun kawo cewa wata dalibar jami'ar Ilorin mai shekaru 20, Sanni Hameedat, ta halaka kanta bayan ta rantawa wani saurayi da suka hadu a dandalin Snapchat kudi N500,000.

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, hukumar kula da dakunan kwanan dalibai masu zaman kansu da take zaune, ta ce Hameedat na cikin yin kwas dinta na neman sanin makamar aiki (SIWES) lokacin da abun ya faru.

Kara karanta wannan

Budurwa Da Ita Kadai Iyayenta Suka Haifa Ta Mutu Kwanaki 12 Bayan Ta Yi Bikin Kammala Jami’a a Facebook

Dalibar jami'ar Ilorin ta halaka kanta
Dalibar Jami’a Ta Sheke Kanta Bayan Ta Rantawa Saurayin Da Suka Hadu a Intanet N500,000 Hoto: University of Ilorin
Asali: Facebook

Hukumar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce:

"An gano dalilin kashe kanta yana da nasaba da bannatar da kudi. Mahaifiyarta ta damka mata amanar wasu makudan kudade a hannunta. Ta hadu da wani saurayi a dandalin Snatchat sannan suka kulla abota.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Lokacin da yaron ya yi ikirarin cewa mahaifiyarsa na fama da cutar sankarar mama kuma yana bukatar N500,000 cikin gaggawa, matashiyar da ta cika da tausayi sai ta yanke shawarar taimaka masa ta hanyar ranta masa rabin kudi miliyan 1 da mahaifiyarta ta bata. Kuma yaron ya yi alkawarin biyan kudin da ya ranta."

An tattaro cewa lokacin da mahaifiyarta ta bukaci a dawo mata da kudin, sai matashin ya toshe duk wasu hanyoyin da zai sada shi da ita.

Wannan al'amari ya sanya ta shiga cikin damuwa matuka, wanda hakan ya sa ta nemi rance daga wurare daban-daban domin cika N500,000 da babu.

Kara karanta wannan

Gambo Haruna: Bakanuwa Mai Marayu 6 Da Ke Sana’ar Tura Baro

Domin biyan bashin N500,000 da ta rantar, Hameedat ta yi nasarar hada N450 daga manhajar daukar bashi sannan ta hada da N50,000 da take tarawa, rahoton Vanguard.

Yadda daliba ta sha maganin kashe kwari

Hukumar makarantar ta kuma bayyana cewa dalibar ta sha maganin kashe kwari ne da daddare.

Abokiyar zamanta, wacce ta yi bacci da wuri, ta farka da tsakar dare kawai sai ta ga Hameedat cikin mawuyacin hali, tana fidda kumfa ta baki da kuma amai.

"Abokiyar zaman tata ta nemi a kawo masu dauki, sannan aka kwashe ta zuwa UITH kafin aka sanar da mutuwarta," inji sanarwar.

Sai dai kuma, ba a samu jin ta bakin shugaban harkokin dalibai da shugaban kula da harkokin jami'ar ba saboda suna halartan taron yaye dalibai.

A halin da ake ciki, shugaban dalibai, Ologundudu Adesunkanmi, ya tabbatar da lamarin, inda ya tabbatar da jawabin hukumar kula da dakunan daliban.

Kara karanta wannan

Kujerar Mataimakin Gwamnan APC Na Tangal-Tangal, Majalisa Ta Tabbatar da Shirin Tsige Shi

Ya ce:

"Shugaban Jami’ar, Shugaban Harkokin Dalibai suna da masaniya kan lamarin, kuma sun sanar da hukumar da ya kamata don fara cikakken bincike kan lamarin. Abin takaici ne yadda jama’ar jami’ar suka rasa ta, ta irin wannan mummunan yanayi."

Kotu ta yankewa masu asirin kudi 5 hukuncin shekaru 12 a gidan yari, ta saki boka

A wani labari na daban, wata kotu a Minna, jihar Neja, ta yanke wa wasu mutane biyar hukuncin shekaru 12 a gidan yari kan tono kan wani mutum daga makabarta.

An tattaro cewa sun yi niyan kai a wani boka da ya bukaci su kawo kan don yi masu asirin kudi ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng