Jerin Nade-Naden Shugaba Tinubu Da Su Ka Jawo Kace-Nace a Tsakanin Al’umma

Jerin Nade-Naden Shugaba Tinubu Da Su Ka Jawo Kace-Nace a Tsakanin Al’umma

FCT, Abuja – A kwanakin nan Shugaba Tinubu ya yi wasu nade-nade a hukumomi daban-daban da su ka jawo cece-kuce daga bangarori da daman a kasar.

Yayin da dama daga cikin mukaman shugaban su ka samu yabo, wasu daga daga ciki kuma sun samu fallasa da kushewa bayan nadin na su, Legit ta tattaro.

Jerin mukaman da Tinubu ya nada da su ka jawo kace-nace a Najeriya
Nade-Naden Shugaba Tinubu da Su Ka Jawo Matsala. Hoto: @realFFK/@hanneymusawa.
Asali: Twitter

Korafin da ake samu ya bambanta yayin da wasu ake duba cancantarsu da mukamin, wasu kuma yanayin yadda mutane ke kallonsu ne ta jawo matsalar.

Legit Hausa ta tsamo muku wasu daga cikin mukaman da aka yi ko kuma ake ci gaba da cece-kuce a kansu:

Ola Olukoyede – Shugaban Hukumar EFCC

A ranar Alhamis 12 ga watan Oktoba, Tinubu ya nada Ola Olukoyede a matsayin shugaban hukimar EFCC don maye gurbin Abdulrasheed Bawa da aka dakatar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shetty, El-Rufai da Sauran Mutum 5 da Tinubu Ya Ba Mukamai, Sai Ya Dawo Ya Karbe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nadin ya jawo kace-nace musamman daga masana shari’a inda su ke kokwanton ko ya cancanta da mukamin duba da dokokin hukumar.

Dokar hukumar ta fayyace cewa dole shugaban hukumar ya kasance ya na da kwarewa a aikin na tsawon shekaru biyar kuma dole ya kasance jami’in tsaro ko mai ritaya.

Tola Odeyemi – Shugabar Hukumar NIPOST

Har ila yau, nadin Tola a ranar Juma’a 13 ga watan Oktoba ya samu tarnaki musamman daga ma’aiktarsa.

Hukumar a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa an mayar da tsohon shugabanta, Adeyemi Adepoju inda ta yi watsi da sanarwar hadimin shugaban kasa, Ajuri Ngelale.

A ranar Litinin, ma’aikatan hukumar sun fantsama zanga-zanga a ofishin hukumar don kin amincewa da nadin Tola a matsayin shugaba, cewar New Telegraph.

Imam Ibrahim Kashim – Shugaban Hukumar FERMA

Nadin Imam mai shekaru 24 a matsayin shugaban hukumar FERMA ya samu yabo daga wasu mutane a kasar ganin yadda ya ke da karancin shekaru.

Kara karanta wannan

Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon DG Na Ofishin Kasafin Ƙuɗin Ƙasa Ya Rasu

Sai dai wasu kuma sun soki nadin da cewa kawai don dan babban mutum ne a siyasa ne shiyasa ya samu mukamin yayin da wasu ke cewa ba shi da kwarewar rike wannan hukumar.

Dele Alake - Ministan Albarkatu

Nadin Alake ya jawo kace-nace inda wasu ke ganin ba shi da kwarewa a wannar ma’aikata ganin cewa ya fi kwarewa ta fannin yada labarai.

Alake ya rike kwamishinan yada labarai a jihar Legas wanda na hannun Shugaba Tinubu ne tuntuni.

Hannatu Musawa – Minstar Al’adu da Adabi

Nadin Musawa wacce har yanzu ta ke bautar kasa ya bar baya da kura inda wasu ke ganin nadin nata ya sabawa doka.

Daraktan yada labarai a hukumar NYSC, Eddy Megwa ya bayyana mukamin yayin da ta ke bautar kasa a matsayin sabawa dokar hukumar.

Falana ya soki Tinubu kan nadin Shugabannin EFCC, ICPC

A wani labarin, Lauya Femi Falana ya soki Tinubu kan nadin shugabannin hukumomin EFCC da ICPC daga yanki daya.

Kara karanta wannan

Badakalar Kwangila: Shugaban EFCC Ya Tona Asiri Kan Asarar da Najeria Ta Yi Cikin Shekaru 3 Na Buhari

Falana ya ce hakan rashin adalci ne da kuma saba doka inda ya ce dole a raba tsakanin Kudu da Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.