EFCC: Mutane Sun Yi Zanga-Zanga a Majalisa Saboda Nadin Shugaban da Aka Yi
- Kungiyar Centre for Democracy & Human Rights (CEDEHUR) ta na yaki da nada Olu Olukoyede ya zama shugaban hukumar EFCC
- Sakataren wannan kungiya mai zaman kan ta ya fadawa majalisar dattawa cewa tantance wanda aka turo zai zama sabawa doka
- Kwamred Adebayo Ogorry ya hakikance cewa doka ba ta ba Ola Olukoyede damar rike EFCC ba domin ba jami’in ‘dan sanda ba ne
Abuja - A daidai lokacin da majalisar dattawa ta ke shirin tantance wadanda za su shugabanci EFCC, sai aka ji wasu su na adawa da hakan.
Business Day ta ce an wasu ba su goyon bayan Ola Olukoyede da Muhammad Hammajoda su jagoranci hukumar yaki da rashin gaskiyar.
Wata kungiya mai suna 'Centre for Democracy and Human Rights' da mutanenta sun fito karara, su na adawa da nadin Olu Olukoyede a EFCC.
"Za a sabawa dokokin EFCC" - CEDEHUR
‘Yan kungiyar sun gudanar da zanga-zanga, su na zargin an sabawa doka wajen nada wanda zai canji Abdulrasheed Bawa a hukumar ta EFCC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakataren kungiyar na kasa, Kwamred Adebayo Ogorry yake cewa abin da Bola Ahmed Tinubu ya yi, ya ci karo da rantsuwar karbar mulki.
Adebayo Ogorry ya na ganin idan nadin ya tabbata, an yi wa dokoki hawan kawara.
Shugabancin EFCC sai 'Dan sanda
Ikirarin da jagoran na kungiyar CEDEHUR ya ke yi shi ne zaman lauyan shugaban EFCC zai ci karo da sashe na dokar da ta kafa Hukumar.
Da yake fassara dokar, Ogorry ya ce EFCC ba ta fararen hula ba ce, don haka ake bukatar wanda zai zama shugabanta ya kasance ‘dan sanda.
Idan aka tabbatar da tsohon sakataren, CEDEHUR ta na ganin an bude kofar saba doka. Zargin da fadar shugaban kasa ta musanya tuni.
"Aikin Shugaban kasa Bola Tinubu wajen nada Mr Olukoyede a babban ofis mai dauke da nauyi sosai na shugaban EFCC ya ci karo da tanadin dokokin majalisa kuma ya sabawa rantsuwar da ya yi a ranar 29 ga watan Mayun 2023, na cewa zai kare dokokin kasar nan."
- Adebayo Ogorry
Rahoton da ya fito dazu kuwa shi ne Majalisar dattawa za ta tantance sabon shugaban hukumar EFCC yau Laraba duk da surutun jama’a.
Tantancewar na zuwa ne bayan Bola Tinubu ya nemi majalisar ta amince da naɗin da ya yi, wanda ya jawo abin magana ta fuskar dokar kasa.
Asali: Legit.ng