Gwamnatin Jihar Ondo Ta Musanta Batun Sake Fitar da Gwamna Akeredolu Kasar Waje Neman Lafiya
- Har yanzu akwai rashin tabbas dangane da lafiyar gwamna Rotimi Akeredolu duk da tabbacin da sansaninsa ya sha bayar wa na cewa lafiyarsa ƙalau
- Halin rashin lafiyar gwamnan na jihar Ondo ya fara yawo a kafafen yaɗa labarai cikin watanni huɗu da suka gabata
- A wannan makon ne wani rahoto ya bayyana cewa akwai shirye-shiryen mayar da gwamnan ƙasar Jamus domin har yanzu yana bukatar kulawa sosai, sansanin gwamnan ya mayar da martani
Akure, jihar Ondo – Gwamnatin jihar Ondo ta bayyana rahoton cewa gwamna Rotimi Akeredolu zai koma ƙasar Jamus domin jinya a matsayin wanda babu gaskiya a cikinsa.
A cewar Vanguard, wata sanarwa a ranar Talata, 17 ga watan Oktoba, ta hannun babban sakataren yaɗa labarai na Akeredolu, Richard Olatunde, ta ce "rahoton wasu ƴan siyasa ne suka kitsa shi waɗanda ke cigaba da jin zafi na rashin nasarar da suka yi.
'Akwai mugun shiri akan Akeredolu': gwamnatin Ondo
Olatunde ya ƙara da cewa labarin da ake ta yadawa ba shi da tushe ballantana makama, kuma tunanin kawai wasu miyagun ƴan siyasa ne, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da hakan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya buƙaci jama'a da su yi watsi da rahoton ƙaryar sannan kada su yarda ƙarairayin da ake yaɗa wa a kan gwamnan su yi tasiri a kansu.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
“Yayin da al'ummar jiha ke farin ciki da dawowar gwamnan lafiya daga hutun jinya, waɗannan ƴan siyasan da ke cikin ruɗani sun kasance cikin dare suna cizon yatsa saboda nadamar rashin nasarar mummunan shirin da suka yi."
"A gare mu, mun himmatu wajen magance matsalolin da al'ummar jihar waɗanda ke ci musu tuwo a ƙwarya. Wannan ne ya sa aka fi bayar da fifiko kan cigaba a ƙarƙashin gwamnatin Akeredolu."
Ganduje Ya Gana Da Yan Majalisar Jiha
A wani labarin kuma, shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya gana da fusatattun ƴan majalisar dokokin jihar Ondo.
Ganduje ya gana da ƴan majalisar dokokin ne domin magance rigimar da ake yi kan batun tsige mataimakin gwamnan jihar daga muƙaminsa.
Asali: Legit.ng