Majalisar Dattawa Za Ta Tantance Olukoyede a Matsayin Sabon Shugaban EFCC
- Majalisar dattawa za ta tantance sabon shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon EFCC ta EFCC
- Majalisar za ta tantance Olanipekun Olukoyede a matsayin sabon shugaban hukumar biyo bayan naɗin da aka yi masa
- Naɗin nasa dai ya jawo ƙorafe-ƙorafe kan cewa ya saɓa dokar hukumar FCC, sai dai fadar shugaban ƙasa na son a tabbatar da shi a matsayin sabon shugaba
FCT, Abuja - A yayin da ake cigaba da kamun ƙafa, majalisar dattawa a yau (Laraba) za ta tantance Olanipekun Olukoyede a matsayin sabon shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon kasa ta EFCC.
Shugaban Bola Tinubu ya aike da wasiƙa zuwa ga shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio a makon da ya gabata, inda ya nemi a amince da Olukoyede a matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na tsawon shekara huɗu.
Naɗin Olukoyede na zuwa ne kusan watanni huɗu bayan dakatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban EFCC. Daga baya tsohon shugaban ya yi murabus.
Sai dai zaɓin Olukoyede a matsayin shugaban hukumar EFCC, ya janyo korafe-korafe daga wasu mutane, inda suka yi zargin cewa naɗin na sa ya saɓawa dokar hukumar FCC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An shawo kan sanatoci su amince da Olukoyede
Jaridar The Nation ta ce a daren jiya ne dai fadar shugaban ƙasa da shugabannin majalisar dattawa suka fara aiki domin shawo kan sanatocin da ke adawa da naɗin nasa.
Majiyoyin da ke kusa da majalisar dattawa sun bayyana cewa an gayyaci Olukoyede, tsohon sakataren hukumar ne domin tantancewar bayan an yi masa binciken tsaro.
Ɗaya daga cikin majiyoyin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa:
"An shirya komai domin tantance sabon shugaban EFCC. Bayan samun wasiƙa daga shugaban ƙasa Bola Tinubu, majalisar dattijawa ta gayyaci Olukoyede domin fuskantar mambobinta kan manufofinsa da kuma dalilin da ya sa ya cancanci a amince da shi."
"Sanatoci daga nan za su tattauna da shi kan shirye-shiryen yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma dalilin da ya sa yake da wuya a magance cin hanci da rashawa a ƙasar nan.”
Wanene Olanipekun Olukoyede
Rahoto ya zo kan bayani dangane da Olanipekun Olukoyede, wanda Shugaba Tinubu ya naɗa a matsayin sabon shugaban hukumar EFCC.
Olukoyede haifaffen jihar Ekiti ne a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, kuma zai zama ɗan Kudu na farko da ya shugabanci hukumar idan majalisar dattawa ta amince da naɗin da aka yi masa.
Asali: Legit.ng