Tinubu Ya Nada Adamu Aliyu a Matsayin Sabon Shugaban Hukumar ICPC

Tinubu Ya Nada Adamu Aliyu a Matsayin Sabon Shugaban Hukumar ICPC

  • Shugaba Tinubu ya nada Dakta Adamu Aliyu a matsayin sabon shugaban hukumar ICPC
  • Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya bayyana a cikin wata sanarwa a yau Talata
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan ya nada Ola Olukoyede a matsayin shugaban Hukumar EFCC

FCT, Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya nada sabon shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci ta ICPC.

Tinubu ya nada Dakta Musa Adamu Aliyu a matsayin sabon shugaban Hukumar ta ICPC yayin da ya kuma nada Mista Clifford Okwudiri a matsayin sakataren hukumar.

Tinubu ya nada Adamu Aliyu shugaban hukumar ICPC
Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar ICPC. Hioto: @iamAhmadOlolu, @officialABAT.
Asali: Twitter

Yaushe Tinubu ya nada Adamu Aliyu shugaban ICPC?

Hadimin shugaban a bangaren yada labarai Ajuri Ngelale shi ya bayyana haka a yau Talata 17 ga watan Oktoba a cikin wata sanarwa, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

"Yarbawa Kirista Ake Fifitawa": MURIC Ta Soke Tinubu Kan Nade-Nadensa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ajuri ya ce nadin sabbin mukaman ya ta’allaka ne ga majalisar Dattawa bayan sun tantance su, Daily Trust ta tattaro.

Sanarwar ta ce:

"Bisa ga karfin iko na shugaban kasa sashi na 3 (6) na hukumar yaki da cin hanci, ICPC na shekarar 2000 wanda ya ba shi damar kawo sauyi a yaki da cin hanci.
"Shugaba Tinubu ya amince da nadin sabbin shugabannin hukumar ICPC wanda zai ta'allaka ga tantancewar majalisar Dattawa kamar haka:
"Dakta Adamu Aliyu - shugaban Hukumar ICPC.
"Mista Clifford Okwudiri - Sakataren hukumar ICPC."

Waye Adamu Aliyu da Tinubu ya nada shugaban ICPC?

Dakta Musa Aliyu ya kammala digiri dinsa na farko da na biyu, sannan kuma ya na da digirin digir-gir a bangaren shari'a.

Shugaba Tinubu ya bukaci sabbin shugabannin da aka nada da su yi aiki tukuru ba tare da tsoro ba ko kuma son kai yayin gudanar da aikinsu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Aike da Wasika Ga Majalisar Dattawa Kan Shugaban EFCC

Wannan nadin na Dakta Adamu Aliyu na zuwa ne kwanaki kadan bayan Tinubu ya nada Ola Olukoyede a matsayin shugaban Hukumar EFCC.

Lauyoyi da dama sun kushe nadin na Ola inda su ka ce Tinubu ya saba dokar hukumar wurin nada shi shugaban Hukumar EFCC.

Falana ya soki Tinubu kan nadin shugabannin EFCC, ICPC

A wani labarin, shahararren lauya, Femi Falana ya caccaki Bola Tinubu kan nadin shugaban Hukumomin EFFC da ICPC daga yanki daya.

Falana ya bayyana cewa hakan sabawa doka ce da kuma rashin adalci dole daya ya fito daga yankin Kudu daya kuma Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.