Yan Bindiga Sun Halaka Yan Sakai Mutum 9 a Jihar Bauchi

Yan Bindiga Sun Halaka Yan Sakai Mutum 9 a Jihar Bauchi

  • Ƴan bindiga sun halaka ƴan sakai mutum tara a wani mummunan kwanton ɓauna da suka yi musu a jihar Bauchi
  • Ƴan sakan dai sun fita aikin sintiri ne domin kakkaɓe miyagun ƴan bindiga lokacin da lamarin ya auku
  • A yayin kwanton ɓaunan dai, rayukan ƴan sakai mutum tara ne suka salwanta ya yin da wasu da dama suka samu raunika

Jihar Bauchi - Ƴan bindiga sun kashe ƴan sakai mutum tara waɗanda aka fi sani Ƴan Ba ​​Beli a ƙauyen Gamji da ke ƙaramar hukumar Ningi ta jihar Bauchi.

Wani ɗan kungiyar ƴan sakan da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a lokacin da ƴan sakan suka fita sintiri, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ysn Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Jihar Arewa, Sun Salwantar da Rayukan Bayin Allah

Yan bindiga sun halaka yan sakai a Bauchi
Yan bindiga sun halaka yan sakai a jihar Bauchi Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Majiyar ta bayyana cewa ƴan bindigan sun yi wa tawagar ƴan sakan kwanton ɓauna inda suka kashe mutum tara tare da raunata wasu da dama.

Yadda lamarin ya auku

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Lokacin da ƴan sakan suka shiga cikin kwanton ɓaunan, ƴan bindigan sun buɗe wuta da manyan muggan makamai inda suka yi galaba a kan ƴan sakan, inda a nan take suka kashe mutum tara daga cikinsu tare da jikkata wasu."

Ya bayyana cewa an gano gawarwakin mutanen da aka kashe a safiyar ranar Litinin kuma an binne su a wurin da lamarin ya faru kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, rahoton The Punch ya tabbatar.

Wane martani hukumomi suka yi?

Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Ningi, Ibrahim Mato wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya bayyana kisan a matsayin rashin imani, yana mai cewa gwamnati za ta cigaba da yin duk mai yiwuwa domin kare rayuka da dukiyoyi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Dakarun Sojoji Sun Ceto Daliban Jami'ar FUGUS, Bayanai Sun Bayyana

Kokarin jin martanin rundunar ƴan sandan jihar Bauchi bai yi nasara ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 3 a Benue

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai wani mummunan hari a ƙauyen Imaton na ƙaramar hukumar Logo ta jihar Benue.

Ƴan bindigan waɗanda suka addabi mutanen yankin da kai hare-haren ta'addanci, sun salwantar da rayukan mutum uku a sabon harin da suka kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng