Gwamna Fintiri Ya Ja Kunnen Kwamishinoninsa Kan Cin Hanci da Rashawa

Gwamna Fintiri Ya Ja Kunnen Kwamishinoninsa Kan Cin Hanci da Rashawa

  • Gwamnan jihar Adamawa ya shirya sa ƙafar wando ɗaya da duk wani daga cikin muƙarraban gwamnatinsa da aka samu da laifin cin hanci da rashawa
  • Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya bayyana cewa duk wanda aka samu da laifin hakan zai gurfana a gaban hukuma
  • Fintiri ya bayyana hakan ne dai wajen wani taron bita na kwanaki uku da aka shiryawa kwamishinoni da manyan sakatarori na jihar

Jihar Adamawa - Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya sanar da kwamishinoninsa da manyan sakatarori a jihar cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci cin hanci da rashawa ba.

Gwamna Fintiri ya bayyana cewa duk wani daga cikin muƙarraban gwamnatinsa da aka kama da laifin cin hanci da rashawa, ba wai kawai za a kore shi ba ne, sai an gurfanar da shi a gaban hukuma, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Kujerar Mataimakin Gwamnan APC Na Tangal-Tangal, Majalisa Ta Tabbatar da Shirin Tsige Shi

Gwamna Fintiri ya gargadi kwamishinoni
Gwamna Fintiri ya gargadi kwamishinoni kan cin hanci da rashawa Hoto: Ahmadu Umaru Fintiri
Asali: Twitter

Da yake jawabi a ranar Talata, 17 ga watan Oktoba, yayin wani taron bita da aka shirya wa kwamishinoni da manya sakatarori, Fintiri ya bukaci manyan jami'an gwamnatin da su kasance masu taka tsan-tsan da dukiyar gwamnati da mutunta lokaci.

Wacce shawara gwamnan ya ba su?

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ku kasance masu taka tsan-tsan da kuɗaɗe. Idan akwai abin da za mu iya yi a N1, mu yi shi a N1. Kuma ku yi amfani da lokacinku yadda ya dace. Kada mu kasa kawo sauye-sauye bayyanannu a wuraren da muke aiki."

Ya kuma shawarci muƙarraban gwamnatin nasa da su kasance masu ƙan-ƙan da kai wajen gudanar da ayyukansu ga al'umma.

"Dukkanmu masu kula da aikin mutane ne. Ba mu fi kowa ba face kawai mu masu hidima ne domin gina Adamawa." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Arewa Ya Bayyana Abin da Zai Yi da Kudaden da Tsohon Gwamna Ya Sace

Taron na kwanaki 3, wanda aka shirya wa kwamishinoni 24 da manyan sakatarori 31, an tsara shi ne domin gabatar da ƙasidu 10, inda ƙasida ta farko wacce ta yi magana a kan samar da tsare-tsare da aiwatarwa, mataimakin shugaban jami'ar Modibbo Adama da ke Yola, ya gabatar da safiyar ranar Talata.

Shugaba Tinubu Ya Kaddamar da Tallafin Rabon Kudi

A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ƙaddamar da tallafin rabon kuɗi ga gidaje miliyan 15.

Ƴan Najeriya miliyan 62 ne za su amfana da tallafin domin rage musu raɗaɗin halin matsi da ƙuncin rayuwar da ake ciki a ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng