“Mayya Ce”: Wani Mutum Ya Tsorata Yayin da Ya Yada Bidiyon Halittar Da Ya Gani a Gefen Janaretonsa

“Mayya Ce”: Wani Mutum Ya Tsorata Yayin da Ya Yada Bidiyon Halittar Da Ya Gani a Gefen Janaretonsa

  • Wani matashi dan Najeriya ya garzaya shafin soshiyal midiya don baje koli wani abun mamaki da ya gani a gidansa
  • Yana shirin kunna janaretonsa ne lokacin da ya lura da wata bakuwar halitta a gefen injin din tana kallon shi
  • Yayin da wasu suka yi ikirarin cewa mujiya ce, wasu sun bukaci da ya kara taka-tsantsan domin tana iya kasance 'mayya'

Wani matashi dan Najeriya ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya kan wata halitta da ya gani a gefen janaretonsa.

Da ya garzaya shafinsa na TikTok, mutumin mai suna @timitrey, ya yada bidiyon halittar, cewa yana shirin kunna janaretonsa ne ya ci karo da ita.

Matashi ya ga tsuntsu mai ban tsoro a janaretonsa
“Mayya Ce”: Wani Mutum Ya Tsorata Yayin da Ya Yada Bidiyon Halitta Da Ya Gani a Gefen Janaretonsa Hoto: @timitrey
Asali: TikTok

Matashin ya ce ya tsorata matuka sannan ya nemi a kawo masa agaji. A wani bidiyo da ya biyo baya, wani mai karfin hali ya bayyana a wajen sannan ya taimaka wajen korar halittar.

Kara karanta wannan

“Yi Mun In Maka”: Wata Mata Ta Kashe Miliyoyi Wajen Siyawa Mijinta Kyaututtuka, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Halittar ta yi kama da mujiya

Wani nazari a kan bidiyon ya nuna halittar ta yi kama da mujiya. A cewar Barn Owl Trust, mujiya wasu tsuntsaye ne da ke farauta da kama kananan dabbobi masu shayarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Suna da wasu halaye na musamman wadanda ke taimaka musu wajen farautar abinci da daddare, kamar ji sosai da kuma ikon ganin duk wani motsi da dan karamin haske.

Sai dai kuma, mutane da dama sun ce halittar wata 'mayya' ce ko kuma wani surkulle.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun bayyana ra'ayinsu kan bakuwar halitta

Kingsley ya ce:

"Da ace a turai ne da yanzu sun dauke ta sun fara kiwonta amma tunda a Najeriya ce ba za ka iya yarda da komai ba faaaa."

DONBABA ya ce:

"Baaba wannan tsuntsun na da tsada sosai a kasuwa.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Fusata Ta Juye Ruwa a Gadonsu Na Sunna Saboda Miji Ya Ki Siya Mata Gashin Kanti

"Muna kiranta da Owiwi."

Ayibatarinelson ya ce:

"Abu kadan Yesu me ya faru????? Wato mujiya ba za ta iya shakatawa a yankinku ba kuma ko????"

fashipegbenga ya ce:

"Wannan tsuntsun zai iya kai wa miliyan 50 ku je ku tambayi Ola of Lagos."

Yan Najeriya sun yi tururuwan zuwa diban mai daga wata tanka da ta fadi

A wani labari na daban, mun ji cewa wani bidiyo da ya yadu a TikTok ya nuna yadda wasu yan Najeriya suka sanya kansu cikin kasada don diban man fetur da ke zuba a bakin hanya.

Wani bidiyo mai tsawon sakan 44 da @korasfiregrill ya wallafa ya nuna cewa wata motar tanka ta fadi a babban hanya sannan abun cikinta ya dungi kwarara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng