Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mata 27 da Yara 2 a Kudancin Kaduna
- Miyagun 'yan bindiga sun yi awon gaba da mata 27 da kananan yara huɗu a kudancin jihar Kaduna
- Ɓangaren mata na ƙungiyar SOPAPU sun bayyana cewa lamarin ya faru ne ranar 2 ga watan Oktoba, 2023
- Ta ƙara da cewa yan bindigan jeji sun tarwatsa kauyuka da dama, sun kashe mutane kuma sun kama na kamawa
Jihar Kaduna - Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa akalla mata 27 da kananan yara huɗu da ake zargin 'yan bindiga sun yi garkuwa da su a kudancin jihar Kaduna.
Ɓangaren mata na ƙungiyar mutanen kudancin Kaduna, SOPAPU, ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, 16 ga watan Oktoba, 2023.
Ƙungiyar ta yi kira ga mahukunta sun taimaka su yi duk mai yiwuwa wajen ceto waɗan da ke hannun 'yan ta'adda.
Kodinetan mata ta ƙungiyar SOPAPU, Misis Jemutu Katarma, ta ce wannan sabon lamarin na sace mata 27 da yara huɗu ya faru ne ranar 2 ga watan Oktoba, 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta kuma bayyana cewa har yanzun waɗanda aka sace suna hannun masu garkuwa da mutane, rahoton Ripples ya tattaro.
Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka da dama
Sanarwan ta ƙara da bayanin cewa 'yan ta'addan sun tashi ƙauyuka da dama a yankin kudancin Kaduna yayin da ɗaruruwan jama'a suka rasa matsugunan su.
A cewar Katarma, a cikin kananan hukumomi 12 da ke kudancin Kaduna, uku ne kawai ba su fuskanci tashin hankali da ta'addancin yan bindiga ba.
Kodinetan ta ce musamman yan fashin daji, mahara makiyaya domin dubbannin mutane sun rasa rayukansu, an ƙona gidaje yayin da ɗaruruwa kuma aka yi garkuwa da su.
A halin da ake ciki, babu wani tabbaci a hukumance ko dai daga jihar ko kuma rundunar ‘yan sandan, kamar yadda Tribune ta rahoto.
Dakarun Sojoji Sun Samu Nasara Kan Yan Bindiga, Sun Ceto Mutane da Dama da Suka Sace a Arewacin Najeriya
Kuma da aka tuntuɓi jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Kaduna, Mansur Hassan, domin jin ta bakinsa ta wayar tarho amma kuma ba ta shiga ba.
Yan Bindiga Sun Halaka Basarake, Sun Yi Awon Gaba da Mutane da Yawa a Niger
Kuna da.labarin Yan bindiga sun yi ajalin Basarake, sun tattara jama'a sun yi awon gaba da su a ƙauyukan jihar Neja ranar Talata da daddare.
Rahotanani daga mazauna yankin sun nuna cewa maharan sun haɗa harda mata sun yi garkuwa da su, sun sace dabbobi.
Asali: Legit.ng