Hukumar EFCC Ta Cafke 'Mama Boko Haram' da Wasu Mutum 2 Kan Badakalar Naira Miliyan 150
- Hukumar EFCC ta gurfanar da wasu mutane uku da ake zargi da badakalar Naira miliyan 150 a jihar Borno
- Wadanda ake zargin, Aisha Alkali Wakil wacce aka fi sani da 'Mama Boko Haram' da kuma Tahiru Saidu Daura da Prince Lawal Shotoye
- Hukumar ce ta bayyana haka a shafinta na Twitter a yau Litinin 16 ga watan Oktoba
FCT, Abuja – Hukumar Yaki da Cin Hanci a Najeria (EFCC) ta kama Aisha Wakil wacce aka fi sani da 'Mama Boko Haram' kan badakalar Naira miliyan 150.
Hukumar ta bayyana haka ne a shafinta na Twitter a yau Litinin 16 ga watan Oktoba, Legit ta tattaro.
Meye EFCC ke zargin Mama Boko Haram da saura?
Sanarwar ta ce an kama Aisha da wasu mutane biyu da su ka hada da Tahiru Saidu Daura da Prince Lawal Shoyode zuwa babbar kotun jihar Borno kan zargin badakalar Naira miliyan 150.
Yadda Yan Sanda Suka Kama Fasto da Wasu Mutum 3 da Kokon Kan Dan Adam, Sun Fadi Abin da Za Su Yi da Shi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce:
“Hukumar Yaki da Cin Hanci, EFCC ta kama Aisha Alkali Wakil da aka fi sani da 'Mama Boko Haram' tare da Tahiru Saidu Dauda da Prince Lawal Shoyode.
“An gurfanar da su a gaban Babbar kotun jihar Borno da ke Maiduguri kan hadin baki da kuma sata na Naira miliyan 150.”
Meye martanin wadanda Hukumar EFCC ke zargi?
Wannan laifi ya sabawa dokar kasa sashi na 320 na kundin laifuka da hukunci na jihar Borno.
Wadanda ake zargin ba su amince da laifin da ake zarginsu a kai ba yayin da aka karanto musu a gaban kotun.
Lauyoyin hukumar sun bukaci Alkalin kotun ya saka ranar da za a ci gaba da shari’ar.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Fadawu ya dage sauraran karar inda ya umarci a ci gaba da tsare wadanda ake zargin a gidan kaso.
Tinubu ya nada Ola Olukoyede shugaban EFCC
A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya nada Ola Olukoyede a matsayin sabon shugaban Hukumar EFCC.
OLa ya kasance kwararren lauya da ya shafe shekaru a hukumar kuma zai yi wa'adin shekaru hudu bayan majalisa ta tantance shi.
Wannan na zuwa ne bayan Tinubu ya dakatar da tsohon shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa bayan hawanshi mulki.
Asali: Legit.ng