Cakwakiya: Tinubu Ya Maida Shugaban NIPOST Kan Mukaminsa Bayan Tsige Shi

Cakwakiya: Tinubu Ya Maida Shugaban NIPOST Kan Mukaminsa Bayan Tsige Shi

  • Sunday Adepoju da aka fitar da sanarwa a makon jiya cewa an tsige shi daga shugabancin NIPOST ya dawo kan kujerarsa
  • Da farko sanarwa ta fito daga fadar shugaban kasa cewa Bola Tinubu ya nada Tola Odeyemi ta jagoranci Hukumar NIPOST
  • Kwatsam sai ga jawabi cewa har gobe Adepoju ya na kan kujerarsa, shugaban Najeriya ya yarda ya cigaba da rike mukamin

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta kuma nada Sunday Adepoju a matsayin shugaban hukumar NIPOST ta kasa a Najeriya.

Tribune ta ce NIPOST ta tabbatar da haka a wani jawabi na musamman da ta fitar a ranar Asabar, 14 ga watan Oktoba 2023.

Sanarwar ta ce Sunday Adepoju zai cigaba da zama a kujerar da ya ke kai tun 2022.

Tinubu
Tsofaffi da sababbin shugabannin NIPOST, NIGCOMSAT, NCC Hoto: @bosuntijani
Asali: Twitter

Sanarwar da NIPOST ta fitar

"Mista Sunday Adepoju ya na aikawa da godiyarsa ga Shugaba Bola Tinubu da sauran muhimman magoya baya.

Kara karanta wannan

Ma’aikata ba Su Kaunar Shugabar da Tinubu Ya Nada, Sun Hana ta Shiga Ofis

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya dauki alkawarin ribanya kokarin da ya ke yi na daukaka NIPOST zuwa babban hukumar aika sakaonni na zamani
Tare da ganin ya yi daidai da burin Ma’aikatar sadarwa, kirkira da tattalin arziki zamani wajen kawo cigaban tattali."

- Sunday Adepoju

Rudani ya shigo NIPOST

The Cable ta ce an samu rudani a hukumar tarayyar a lokacin da Adepoju ya nuna ba zai sauka daga kujerar da yake rike da ita ba.

Bayan sanar da nadin sababbin shugabannin NIGCOMSAT, NCC da NIPOST, sai Adepoju ya nuna ba zai ba Tola Odeyemi wuri ba.

Mista Adepoju ya hakikance cewa ya na nan kan kujerarsa, har aka fitar da bidiyon isowarsa ofis cikin mota, jama'a na taya sa murna.

NIPOS: Buhari ya kawo Adepoju

Idan za a tuna, a lokacin mulkin Mai girma Muhammadu Buhari aka nada Adepoju, sai yanzu ne yake cika shekara guda a ofis.

Kara karanta wannan

Akwai Yiwuwar Sabon Gwamnan CBN Ya Yi Fatali da Tsare-Tsaren Emefiele da Buhari

Daga cikin nasarorin da NIPOST ta samu cikin shekara guda akwai kirkiro tsarin AVS da samar da motoci da babura domin aiki.

Motocin da za a ba 'Yan majalisa

‘Yan Majalisar tarayya sun ce ba a kan su aka fara rabon motoci ba, kuma ba kyauta ake ba su ba, an rahoto Hon. Akin Rotimi ya na kare su.

Rotimi ya ce Mataimakan Darektoci da manya a gwamnati su na samun motocin ofis, saboda haka bai kamata a hannun ‘yan majalisa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng