Shugaban ’Yan Sandan Najeriya Zai Tafi Amurka Koyon Yaki Da ’Yan Ta’adda Ta Hanyar Zamani

Shugaban ’Yan Sandan Najeriya Zai Tafi Amurka Koyon Yaki Da ’Yan Ta’adda Ta Hanyar Zamani

  • Rundunar 'yan sandan Najeriya za ta samu sabon ilimi nan ba dadewa ba kan yadda za a yaki 'yan ta'adda
  • An tura mukaddashin shugaban 'yan sandan Najeriya Amurka don koyo hanyar yaki da tsagerun 'yan ta'adda
  • An gayyaci kasashe da yawa don halartar taron da ake yi tun ranar 14 ga watan Oktoban da muke ciki

FCT, Abuja - Mukaddashin Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, zai jagoranci tawagar manyan jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya zuwa babbar taron kungiyar shugabannin ‘yan sanda na kasa da kasa na 2023 a San Diego, Carlifornia, Amurka.

Taron, mai taken 'The Real Advantage', an shirya shi ne don samar da dandali mai kima ga shugabannin 'yan sanda da kwararrun jami'ai a duk fadin duniya don aiki tare wajen tabbatar doka da oda a duniya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: ’Yan Sanda Sun Dakile Yunkurin Sace Taragon Jirgin Kasa a Jihar Arewa, Sun Kama Mutum 6

Shugaban 'yan sanda zai tafi Amurka taro
Shugaban 'yan sanda zai tafi Amurka taron karawa juna sani | Hoto: NPF
Asali: Facebook

A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar ranar Lahadi, tuni an fara taron tsakanin ranar 14 zuwa 17 ga watan Oktoba, 2023.

Ya taron zai kasance?

A cewarsa, ana taron ne a babban dakin taro na San Diego, inda manyan baki daga duniya suka hallara don karawa duna sani game da lamarin tsaro, rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana sa ran taron zai fayyace sabbin hanyoyi na zamani don yaki da 'yan ta'adda da kuma wanzar da zaman lafiya a kasashen duniya.

Daga cikin manyan abubuwan da taron zai fi mayar da hankali akai akwai dakile manyan laifukan sata ta yanar gizo da dai sauransu.

Babu kasar da a duniya ta kubuta da manyan laifuka, Najeriya ma na cikin kasashen da ke bukatar hannu don magance tsaro da dukiyar al'umma har ma da rayukansu; musamman Arewa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hankula Sun Tashi Yayin Da Sojojin Isra'ila Suka Kutsa Cikin Zirin Gaza

Barayi sun yi sata a msarauta

A wani labarin, wasu da ake zargin barayi ne sun shiga fadar Olu na garin Ogunmakin da ke karamar hukumar Obafemi-Owode a jihar Ogun, Oba James Sodiya, inda suka yi awon gaba da rawaninsa da sandar sarautarsa.

'Yan barandan sun shiga fadar marigayin Sarkin ne wanda ya rasu kimanin watanni biyu da suka gabata a ranar Alhamis 12 ga watan Oktoban 2023.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ta tabbatar wa manema labarai aukuwar lamarin a birnin Abeokuta, ranar Asabar, 14 ga watan Oktoban 2023, cewar rahoton Daliy Trust.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.