Budurwa Ta Kara Farin Jini Yayin da Ta Yi Kitso ‘Diban Baya’, Ya Yada Bidiyo a TikTok

Budurwa Ta Kara Farin Jini Yayin da Ta Yi Kitso ‘Diban Baya’, Ya Yada Bidiyo a TikTok

  • Budurwa ta ce kwalliya ta biya ta kudin sabulu yayin da kitsonta diban baya ya sa matasa yi mata kallon 'ina ciki'
  • Budurwar da ta yada bidiyo a TikTok ta ce, yanzu ta fahimci maza sun fi kaunar ganin mata masu kitso diban baya
  • Mutane da yawa da suka ga bidiyon sun yi martani, sun ce da gaske maza sun fi son gashin gaske kuma kitso mai sauki

Wata budurwa ta yi farin jini bayan da ta sauya kitsonta zuwa diban baya mai saukin da mata ke yi, maza sun nuna ta yi kyau.

Kyakkyawar budurwar mai suna @fayy_gold ya ce mutane sun nuna alamar sonta da ta shiga kasuwa siyayya da wannan kitso.

A cewarta, maza da mata ne suka nuna sha'awar kitson da ta yi, inda daga baya ta zo kafar TikTok don nunawa mutanen duniya.

Kara karanta wannan

“Yi Mun In Maka”: Wata Mata Ta Kashe Miliyoyi Wajen Siyawa Mijinta Kyaututtuka, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Budurwa ta kara farin jini
Farin jini ya karu daga yin kitso | @fayy_gold
Asali: TikTok

Fayy ta kara da cewa, yanzu dai ta gama gamsuwa cewa, maza sun fi kaunar mata da ke yin kitso mai sauki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jama'a na ta bibiyarta

Ta kuma ce, ta zaci wadanda ke ta bibiyarta a kasuwa na son ta sayi kayansu ne, amma ta gane ba haka bane bayan ta fita daga kasuwa.

A cewarta, wasu neman lambar wayarta ma suka yi domin kulla alaka, kun ga farin jini ya samu kenan.

Daga nan ta ce, ita dai ta gane, daga yanzu babu dogon kitso mai ban wahala, za ta ke yin mai sauki irin wannan diban baya.

Kalli bidiyon:

Martanin mutan TikTok

@Mr Barzz:

"Kowane namiji soyayyarsa ta farko kitso ne. Muna ganinku a haka sai mu tuna soyayyar gaskiya kuma tsantsa. Idan muka ga kashi kai tsayi, fajirci ke zuwa kanmu."

Kara karanta wannan

“Babu Likita”: Mahaukaciya Ta Haifi Kyakkyawan Jinjiri Fari Shar Da Shi, Hotunan Sun Yadu

@Maye Rowland :

"To kusan hakan ne na gaske."

@Morgan Reese:

"A zahiri wannan kalan kitson ya fi makala gashin kanti kyau."

Kwamacala a wani gari da ba na hausawa ba

Wata budurwa 'ysr Najeriya, @Sweet_cocolatey ta bayyana wani hoto wanda ya nuna hahuwarta da wani saurayi a bas.

A rubutun da ta saki a shafin X ranar Jumu'a, 2 ga watan Disamba, 2022, tace matashin saurayin ya dan huta a jikinta a lokacin da suke tsaka da tafiya a motar.

Ta ce abinda mutumin ya yi ya ba ta sha'awa, inda ta nuna cewa ga dukkan alamu ya gaji ne sosai shi yasa ya yi hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.