Wata Mata Ta Fada Ruwa Tsudum Yayin da Dan Achaba Ya Kutsa Kai a Ambaliyar Ruwa, Bidiyon Ya Yadu

Wata Mata Ta Fada Ruwa Tsudum Yayin da Dan Achaba Ya Kutsa Kai a Ambaliyar Ruwa, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani bidiyo mai taba zuciya ya nuna lokacin da wata mata wacce take hanyarta na zuwa wani muhimmin wuri ta fado daga kan babur
  • Matar ta fado ne saboda dan achaban ya shiga wani yanki da ke cike da ambaliyar ruwa sannan ya makale a cikin chabi
  • Bidiyon da ke nuna yadda ta fado daga kan babur din ya yadu kuma ya haifar da martani da dama daga yan TikTok

Wani bidiyo da ke nuna lokacin da wata mata ta fado daga babur sannan ta jike sharkaf da ruwan chabi a hanyar.

A cikin bidiyon da @jab0010 ya wallafa, alamu sun nuna matar na hanyarta ta zuwa wani muhimmin wuri ne lokacin da lamarin ya afku.

Wata mata ta fada a cikin ruwa
Wata Mata Ta Fada Ruwa Tsudum Yayin da Dan Achaba Ya Kutsa Kai a Ambaliyar Ruwa, Bidiyon Ya Yadu Hoto: TikTok/@jab0010.
Asali: TikTok

Bidiyon ya nuna yadda dan achaban ya shiga wata hanya da ke cike da ruwa sannan ya yi kokarin kutsa kai ta ko halin 'ka'ka.

Kara karanta wannan

“Babu Likita”: Mahaukaciya Ta Haifi Kyakkyawan Jinjiri Fari Shar Da Shi, Hotunan Sun Yadu

Kokarinsa na tuka babur a hanyar da ke cike da ruwa ya ci tura yayin da ya makale, lamarin da ya yi sanadiyar faduwar matar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin da matar ta fadi ne babur din ya fara tafiya, sannan dan achaban ya janye daga cikin ruwan.

Kayan matar yan jike da ruwan jan kasa. Mutanen da ke wajen sun fasa ihu a lokacin da suka ga abun da ke faruwa.

Bidiyon ya haifar da martani da dama yayin da aka wallafa shi a TikTok.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama'a yayin da wata mata ta fada ruwa daga babur

@favour 281 ta ce:

"Na sani a chan kasar zuciyar wannan dan achaban dariya na son kashe shi."

@emeraldmaish ta yi martani:

"A kodayaushe ku dunga rike rigar dan achaban musamman a irin wannan yanayi. Idan na fadi, tare za mu fadi."

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Fusata Ta Juye Ruwa a Gadonsu Na Sunna Saboda Miji Ya Ki Siya Mata Gashin Kanti

@Julie natsug ta ce:

"Watakila malamar makarantar gwamnati ce."

@AARMY ya ce:

"Matar nan ma na da katon zuciya. Kin ga irin wannan tarin ruwa sannan kika zauna kamar babu abun da ya faru."

@Ronnesskki ta ce:

"Dan achaban zai ce. Kin kai inda za ki sauka. Mun gode da kika hau tare da mu."

Gambo Haruna: Labarin matar da ke tura baro don ciyar da marayunta 6 a Kano

A wani labari na daban, mun ji cewa Gambo Haruna tana fadi tashi don kula da marayu shida da mijinta ya bar mata.

Matar mai matsakaicin shekaru tana siyar da ruwa a baro don kula da yaranta. A kullun ta kan samu N750 zuwa N1,000 kuma a ciki take biyan N150 na hayan baron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng