Arewa Ta Yi Rashi, Mahaifiyar Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawal Ta Kwanta Dama

Arewa Ta Yi Rashi, Mahaifiyar Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawal Ta Kwanta Dama

  • Allah ya yiwa mahaifiyar tsohon shugaban majalisar dattawa rasuwa, jama'a sun taya shi jimami da alhini
  • Manyan jiga-jigan siyasa a Arewacin Najeriya ne suka samu halartar taron jana'izar da aka gudanar a Yobe
  • Al'ummar jihar sun taru don ta'aziyya da kuma bayyana addu'ar Allah ya gafarta mata ya kuma yafe mata

Jihar Yobe - A ranar Lahadi ne tsohon shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan ya jagoranci jana'izar mahaifiyarsa Hajiya Halima (Baba) Ibrahim a garin Gashua da ke karamar hukumar Bade a jihar Yobe.

Hajiya Halima ta rasu ne a ranar Asabar a garin Gashua tana da shekaru 86 a duniya, ta bar ‘ya’ya da jikoki da dama, Leadership ta ruwaito.

An gudanar da jana'izar marigayiyar ne kafin a kai ta makabartar Gashua ta tsakiya a birnin Yobe da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mahaifyar Sanata Ahmed Lawan Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

Sanata Ahmad Lawan ya yi rashin mahaifiyasa
Allah ya yiwa mahaifiyar Ahmad Lawan rasuwa | Hoto: Senator Ahmed Lawan
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka yi jana'izarYadda aka yi jana'izar

Limamin babban masallacin Gashua, Alhaji Ahmad Talba ne ya ja sallar jana'izar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Dubban mazauna mazabarsa da dama sun taru don taya jimami da makokin rashin wannan uwa ga manyan mutane a jihar.

Wasu daga manyan kasa da suka halarci jana'izar sun hada da gwamnan jihar Borno, Babagana Zukum, mataimakin gwamnan Yobe, Idi Barde Gubana da kakakin majalisar jihar Chiroma Mashio.

Sanatoci sun halarci jana'iza

Sauran manyan sun hada da sanata Babangida Hussaini, sanata Kaka Shehu Lawan , Hon. Usman Zannah da kwamishinonin gwamnatin jihar ta Yobe.

Mataimakin gwamnan jihar Yobe ya mika sakon ta'aziyyarsa, inda ya ba sanatan hakuri bisa wannan babban rashi na mahaifiyarsa.

An ba sauran ahali da dangi hakuri da juriyar rashin, fatan Allah ya jikanta ya kuma gafarta mata ya sa ta huta, Amin.

Kara karanta wannan

Hotuna Masu Ban Sha’awa Yayin Da Gwamna Ya Ziyarci Tsohon Telansa Tun Yana Makaranta

An shiga jimamin mutuwar mahaifiyar karamin Shehin Malami

A wani labarin, ana cikin jimami yayin da mahaifiyar Dakta Zakeer wanda aka fi sani da Young Sheikh Zaria ta riga mu gidan gaskiya.

Dakta Zakeer ya bayyana rasuwar mahaifiyar tasa a shafinsa na Facebook a yau Juma’a 29 ga watan Satumba.

Ya ce mahaifiyar tasu ta rasu a cikin dare inda ya bayyana cewa za a yi sallar jana’izarta da misalin karfe 4:30 na yammacin yau Juma’a a Zawiyyar Sheikh Aliyu Mai Yasin a Zaria.

Asali: Legit.ng

Online view pixel