Dakarun Sojoji Sun Ceto Daliban Jami'ar FUGUS da Yan Bindiga Suka Sace
- Dakarun sojojin Najeriya na Operation Hadarin Daji sun samu nasarar ceto ɗaliban jami'ar gwamnatin tarayya ta Gusau (FUGUS) da aka sace
- Dakarun sojojin sun samu nasarar ceto ɗaliban ne bayan sun yi musayar wuta da ƴan bindigan jim kaɗan bayan sun yi awon gaba da ɗaliban
- Luguden wutan da dakarun sojojin suka yi wa ƴan ta'addan ita ta sanya suka ranta ana kare tare da ƙyale ɗaliban da suka sace
Jihar Zamfara - Dakarun sojojin Najeriya sun kuɓutar da ɗaliban jami'ar gwamnatin tarayya ta Gusau (FUGUS) su huɗu da wasu ƴan bindiga suka yi garkuwa da su ranar Asabar, 14 ga watan Oktoba a jihar Zamfara.
PRNigeria ta tattaro cewa an sace ɗaliban ne a ɗakin kwanansu na wajen makaranta da ke unguwar Sabon Gida a ƙarkashin yankin Damba a ƙaramar hukumar Gusau ta jihar Zamfara.
Wata majiyar sirri ta tsaro ta bayyana cewa, a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci da samun kiran gaggawa, dakarun sojojin Operation Hadarin Daji, sun toshe duk wata babbar hanyar fita domin tunkarar ƴan bindigan.
Ta yaya aka ceto ɗaliban?
A kalamansa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Nan da nan dakarun sojojin suka bazama tare da tare dukkanin hanyoyin da ƴan bindigan za su wuce, wanda hakan ya kai ga yin artabu da ƴan ta’addan."
"Luguden wutan da sojoji suka yi ya tilastawa ƴan ta'addan arcewa tare da barin ɗaliban da suka sace."
"A yayin arangama da ƴan ta'addan, biyu daga cikin ɗaliban sun tsere, yayin da sauran biyun mace da namiji jami'an tsaro suka samu nasarar ceto su cikin ƙoshin lafiya."
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar Operation Hadarin Daji, Kyaftin Yahaya Ibrahim, ya tabbatar da samun nasarar ceto ɗaliban, rahoton Leadership ya tabbatar.
Waɗannan ɗaliban da aka ceto dai, ba su daga cikin waɗanda ƴan bindiga suka sace a jami'ar a ranar 22 ga watan Satumban 2023.
Gwamna Ya Bayyana Kudin Fansan da Aka Biya Kafin a Sako Dalibai
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Nasarawa ya bayyana cewa ba a biya ko sisi ba a matsayin kuɗin fansa kafin a sako ɗaliban jami'ar jihar da ƴan bindiga suka sace.
Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana cewa ƙoƙarin da jami'an tsaro suka yi ne ya sanya aka ceto daliban ba tare da biyan ko sisi ba.
Asali: Legit.ng