Shugaba Tinubu Ya Nemi Cin Sabon Bashin Dala Miliyan 400 Daga Bankin Duniya
- Gwamnatin tarayya ta na neman wani sabon bashi daga hannun bankin duniya da sunan a rabawa gidaje marasa karfi
- Iyalai miliyan 15 aka tsara za su amfana da kyautar N25, 000 a duk wata saboda rage radadin cire tallafin man fetur
- Alkaluma sun nuna a shekarar 2023, kasashe uku ne kurum su ka sha gaban Najeriya wajen cin bashin bankin duniya
Abuja - Gwamnatin tarayya ta nemi aron bashin Dala miliyan 400 daga bankin duniya da nufin a rabawa marasa karfi a kasar nan.
A ranar Lahadi, Punch ta kawo rahoto cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta karbo bashin a sakamakon cire tallafin man fetur.
Ganin yadda rayuwa ta kara tsada a dalilin tashin kufin fetur, za ayi amfani da bashin ne domin a rabawa gidaje miliyan 15 a kasar.
Tinubu zai ba gidaje N25, 000
Masu karamin karfi ake sa ran za su amfana da N25, 000 kowace wata. Za a dauki watanni uku; Oktoba zuwa Disamba ana yin rabon.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jawabin da ya gabatar a farkon watan Oktoba, Mai girma Bola Tinubu ya yi alkawari gwamnatinsa za ta rabawa marasa hali kudi.
Baya ga iyalan da za a rika rabawa dubunnan a duk karshen wata domin rage radadi, gwamnati za ta ba ma’aikata karin N35, 000 a wata.
Bashin Najeriya ya karu a 2023
Kafin nan Muhammadu Buhari ya yi nasarar karbo aron $800m daga babban bankin na Duniya domin a tallafawa mutum miliyan 50.
Rahoton da aka fitar ya nuna a cikin shekara guda, Najeriya ta tara bashin fiye da $1bn.
Bayanan da aka samu daga Bankin duniya ya nuna daga Junairu zuwa Yuni, gwamnatin Najeriya ta karbi aron abin da ya kai $14.3bn.
Wanda ta fi kowa cin bashin IDA a shekarar nan ita ce kasar Bangladesh ($19.3bn), sai Indiya ($17.9bn), daga nan sai Fakistan ($16.9bn).
A jeringiyar kasashen da su ka karbi aron bashin kudi a bana, Najeriya ce ta hudu a jerin.
Najeriya ta yi kamu a bankin duniya
Ministan kudi watau Wale Edun ya zama shugaban kungiyar gwamnonin Afrika a bankin duniya, a makon nan aka samu wannan labari.
A shekaru 60 a tarihi sai yanzu ne kujerar nan ta iya isowa kan ‘dan Najeriya, kasar ta na da babbar dama a matsayin shugabar kungiyar.
Asali: Legit.ng