Tinubu Ya Yi Alkawarin Biyan Matasan N-Power Basukan Watanni 8 Nan Kusa
- Yayin masu cin gajiyar N-Power ke korafin basukan da su ke bi, kakarsu ta yanke saka a yanzu
- Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin biyan matasan basukan da su ke bi na tsawon watanni tara
- Manajan shirin, Akindele Egbuwalo shi ya bayyana haka inda ya ce sun samu wasu kudade don biyan basukan
FCT, Abuja – Manajan shirin N-Power a Najeriya, Akindele Egbuwalo ya bayyana cewa sun shirya tsaf don biyan masu cin gajiyar bashin da su ke bi na watanni takwas.
Egbuwalo ya bayyana haka ne a yau Asabar 14 ga watan Oktoba a cikin wata sanarwa inda ya ce sun samu wasu kudade wanda za su yi amfani da su, Legit ta tattaro.
Meye gwamnatin Tinubu ke cewa kan shirin N-Power?
Yayin da ya ke magana da wakilan masu cin gajiyar N-Power, Egbuwalo ya ba da tabbacin cewa za a fara biyan basukan nan ba da jimawa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“Labari mai dadi shi ne an samu wasu kudade kuma za mu fara biya nan ba da jimawa ba.
“Zamu fara biyan basuka ne na masu cin gajiyar N-Power da ke bin gwamnati bashi na watanni takwas nan kusa.”
Ya kara da cewa Minista Betta Edu ta himmatu wurin tabbatar da kawo gyara a cikin shirin da sauran shirye-shirye da su ka shafi ma’aikatar.
Ya karawa matasan kwarin gwiwa da su kara hakuri yayin da su ke ci gaba da kawo gyara a shirin don inganta shi tare da diban miliyoyin ‘yan kasar, The Nation ta tattaro.
Yaushe aka kirkiri shirin N-Power?
Egbuwalo ya ba da tabbacin cewa Shugaba Tinubu ya himmatu wurin dakile talauci a kasar inda ya ce kuma ya kama hanyar cika wannan alkawari.
Tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ce ta kirkiri shirin N-Power inda ake biyan matasa Naira dubu 30 ko wane wata wanda ya rage yawan talauci a tsakanin matasa.
Daga bisani gwamnatin Bola Tinubu ta dakatar da shirin inda ta ce za ta yi bincike kan zargin badakalar kudade a shirin.
Matasan N-Power sun roki Tinubu ya biya su basukan wata 9
A wani labarin, matasa masu cin gajiyar N-Power sun roki Shugaba Tinubu da ya biya su bashin watanni tara da su ke bin gwamnati.
Shugabannin matasan a jihar Gombe, sun bukaci gwamnatin da ta tausaya musu ganin halin matsin da ake ciki a kasar.
Asali: Legit.ng