Yan Sanda Sun Kama Wani Mutum Kan Satar Buhun Shinkafa 47 a Ogun
- Jami'an yan sanda a jihar Ogun sun cika hannu da wani matashi dan shekaru 25
- Ana zargin Damilola Bada da wawure buhun shinkafa 47 mallakin uwar dakinsa wanda farashinsu ya kai miliyan 2.5
- Mai kamfanin Chicken & Co Company ta gano badakalar da aka tafka ne a yayin bincike
Jihar Ogun - Rundunar yan sandan jihar Ogun ta kama wani mutum kan zargin satar buhun shinkafa 47 mallakin uwar dakinsa a yankin Ijebu da ke jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Omolola Odutola, ta gabatarwa manema labarai a ranar Asabar, 14 ga watan Oktoba, jaridar Punch ta rahoto.
Yadda aka kama matashi kan zargin satar buhun shinkafa 47
Wanda ake zargin Damilola Bada, ya sace buhun shinkafa mallakin wani kamfani, Chicken & Co., wanda farashinsa ya kai N2,500,000.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Odutola, mai kamfanin, Oluremi Olabode, ta yi karar lamarin satar kayayyakin da aka yi mata a ofishin Igbeba da ke jihar Ogun wanda ya yi sanadiyar kama Bada mai shekaru 25, rahoton Peoples Gazatte.
Jawabin ya ce:
"A ranar 13 ga watan Oktoban 2023 wata Oluremi Olabode, "mace" mai kamfanin Chicken & Co Company, ta kai karar sata, wanda wani mai kula da shagon ajiyanta mai suna Damilola Bada mai shekaru 25 ke da hannu a ciki.
"Ta zargi Damilola da hada kai da dauran ma'aikata don sace buhun shinkafa arba'in da bakwai, wanda ya kai miliyan biyu da dubu dari biyar.
"Bayan binciken wajen ajiyan, sai mai karar, Oluremi Olabode ta gano satar da aka tafka. Sakamakon haka, DPO na Igbeba ya kama Damilola Bada sannan aka yi masa tambayoyi. Yayin tambayoyin, Damilola ya gaza bayar da gamsasshen bayani game da batan buhun shinkafar da ke karkashin kulawarsa."
Ta yi kira ga al'umma da su sanya idanu sosai sannan su kai karar duk wasu abubuwa da basu gamsu da shi ba garinsu ga ofishin yan sanda mafi kusa.
"Duk dan sanda da ya yi wa yan Najeriya kwacen kudi dan fashi ne", Kakakin yan sanda
A wani labarin, mun ji cewa kakakin rundunar yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana cewa duk jami'in dan sandan da ya nunawa yan Najeriya bindiga domin ya karbi kudi daga hannunsu bai da banbanci da yan fashi, Daily Trust ta rahoto.
Wani dan kasuwar 'crypto' kuma mai fada aji a dandalin X, ya caccaki yan sanda bayan ya zargi jami'an rundunar da kutsa kai cikin gidansa tare da kama shi ta karfi da yaji.
Asali: Legit.ng