Sojoji Sun Ceto Mutum 6 da Aka Yi Garkuwa da Su a Jihar Kaduna

Sojoji Sun Ceto Mutum 6 da Aka Yi Garkuwa da Su a Jihar Kaduna

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar rage mugun iri ta hanyar sheƙe wani ɗan bindiga a jihar Kaduna
  • Dakarun sojojin sun kuma samu nasarar ceto wasu mutum shida da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar
  • Jajirtattun dakarun sojojin sun kuma samu nasarar ƙwato muggan makamai a hannun ƴan bindigan tare da raunata da dama daga cikinsu

Jihar Kaduna - Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su tare da kashe wani ɗan bindiga ɗaya a jihar Kaduna, cewar rahoton The Nation.

Mukaddashin daraktan hulda da jama'a na sojoji runduna ta daya ta Sojojin Najeriya, Laftanal-Kanal Musa Yahaya wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna, ya ce an ceto mutanen ne a ranar Juma'a, 13 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Ana Cikin Murna Yayin da Sojin Najeriya Su Ka Yi Barin Wuta Kan Masu Garkuwa Tare Da Ceto Mutane 17

Sojoji sun halaka dan bindiga a Kaduna
Taoreed Lagbaja, shugaban hukumar sojin kasan Najeriya Hoto: Nigerian Army
Asali: Twitter

Yahaya ya ce cigaba da aikin kakkaɓe ƴan bindiga da dakarun rundunar ke yi, na cigaba da samun sakamako mai kyau, rahoton Vanguard ya tabbatar.

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Rundunar ta yi aiki da sahihan bayanan da ta samu kan sace mutum shida da aka yi a Hayin Tsando a yankin Maraban Jos, a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna."
"Dakarun sojojin sun yi gaggawar yin shiri, suka fara aikin bincike da ceto. Sojojin sun yi arangama da ƴan ta'addan da kuma masu aikata laifuka kuma an yi musayar wuta mai tsanani."
"A yayin farmakin, sojojin sun yi nasarar kuɓutar da wasu mutum shida da aka yi garkuwa da su, sun ƙwace bindigu ƙirar AK 47 guda biyu tare da kashe ɗan bindiga guda ɗaya yayin da wasu da dama suka tsere da raunukan harbin bindiga."

Kara karanta wannan

CSU: Atiku Ya Shiga Matsala, An Roƙi Shugaba Tinubu Ya Cire Masa Lambar Girma Ta GCON

Yahaya ya kuma bukace su da su ci gaba da kai hare-hare har sai an kawar da duk wasu masu aikata laifuka a sashin gaba ɗaya.

Ya kuma yi kira ga ma’aikatan lafiya da su riƙa lura da waɗanda suka samu raunukan harbin bindiga, sannan su kai rahoto ga rundunar sojin Najeriya da sauran jami’an tsaro domin ɗaukar mataki cikin gaggawa.

Ba Batun Sulhu da Yan Bindiga

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da ƴan bindiga ba a jihar.

Gwamnan ya yi nuni da cewa sulhu da ƴan bindiga ba shi da amfani domin ko an yi ba su mutunta alƙawarin da aka yi da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng