Nyesom Wike Ya Bayyana Dalilin Yin Aike a Gwamnatin Tinubu
- Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya ce ya zaɓi yin aiki tare da shugaban ƙasa Bola Tinubu ne saboda kwazonsa da kuma jajircewarsa na siyasa
- Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya kuma bayyana shugabanci a matsayin wani muhimmin al'amari a Najeriya, inda ya jaddada buƙatar samun jagoranci mai nagarta
- Wike ya kuma yi tsokaci kan ƙoƙarin da ya yi na aiwatar da hukumar kula da ma'aikata ta FCT, wacce a baya aka yi watsi da ita
FCT, Abuja - Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya ce ya yanke shawarar yin aiki tare da shugaban ƙasa Bola Tinubu ne saboda kwazonsa da kuma manufofinsa na siyasa.
Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja a ranar Juma'a 13 ga watan Oktoba, inji rahoton TheCable.
Wike na ɗaya daga cikin fitattun jiga-jigan jam'iyyar adawa ta PDP da shugaba Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki ya naɗa muƙamai.
Shugabanci na ɗaya daga cikin matsalolin Najeriya, inji Wike
Wike ya cigaba da cewa ɗaya daga cikin batutuwan da suka addabi Najeriya shine matsalar shugabanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya jaddada buƙatar a gaggauta samar da jagoranci na gari da ɗaukar kwararan matakai domin tunkarar ƙalubalen da al'ummar ƙasar nan ke fuskanta.
Dalilin da ya sa muka aiwatar da hukumar kula da ma'aikata ta FCT, Wike
Lokacin da ya zama ministan babban birnin tarayya, Wike ya ce ya gano cewa an kafa dokar da ta kafa hukumar yi wa babban birnin tarayya hidima amma har yanzu ba a aiwatar da ita ba.
Da ya tsaya tsayin daka, ya kawo maganar ga Shugaba Tinubu, wanda daga baya ya amince da aiwatar da shi.
Wike ya kuma yi kira da a tabbatar da cikakken aiwatar da dokokin da suka samu amincewar majalisar tarayya ta ƙasa da kuma amincewar shugaban ƙasa.
Dalilin Ganawar Wike da Saraki
A wani labarin kuma, kun ji dalilin da ya sanya ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya gana da Bukola Saraki.
Wike ya gana da Saraki ne kan batun nemo wanda zai shugabanci jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na ƙasa.
Asali: Legit.ng