Gwamnan Jihar Ogun Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni
- Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya rantsar da sabbin ƴan majalisar zartaswarsa
- Gwamnan ya buƙaci sabbin masu muƙaman da su yi aiki tuƙuru wajen kawo cigaba ga al'ummar jihar
- Abiodun ya kuma buƙace da kada su yi amfani da muƙaman da suka samu wajen tsangwamar abokan hamayyarsu a jihar
Jihar Ogun - Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, a ranar Juma'a, 13 ga watan Oktoba, ya buƙaci sabbin ƴan majalisar zartaswarsa da aka rantsar da su jajirce wajen ciyar da jihar gaba, cewar rahoton The Punch.
Gwamnan ya buƙaci sabbin ƴan majalisar zartaswar da suka haɗa da kwamishinoni 20 da masu ba da shawara na musamman 22, da kada su tsaya sanya sannan su haɗa ƙarfi da ƙarfe da shi domin inganta rayuwar al'ummar jihar.
Hakazalika, Abiodun ya ce an kammala shirye-shiryen samar da ƙarin ma’aikatu a jihar, inda ya ce idan aka samar da ƙarin ma’aikatun, za a ƙara yawan naɗe-naɗe, duk da cewa ya yi gargaɗin ba kowa ba ne zai samu muƙami a gwamnati ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin rantsar da sabbin kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman a birnin Abeokuta, babban birnin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wacce shawara gwamna Abiodun ya ba su?
Ya kuma buƙaci sabbin masu muƙaman da su taka rawar gani, tare da yin aiki tare domin cigaban jihar ba tare da ɓata lokaci ba, rahoton Thisday ya tabbatar.
Gwamna Abiodun ya gargaɗe su da kada su yi amfani da sabbin muƙaman da suke da su wajen murƙushe abokan hamayyar su, amma su zama wakilai na haɗin kai a mazaɓun su
Ya ce jihar ta samu nasarori da dama a cikin shekaru huɗu da suka gabata, domin haka akwai buƙatar sabbin mambobin majalisar zartaswa su yi aiki tare domin kara zurfafa cigaba a dukkan sassan jihar.
Ba Batun Sulhu da Miyagu
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya nanata aniyarsa ta rashin yin sulhu da ƴan bindiga.
Gwamnan ya bayyana cewa ba zai yi sulhu da ƴan bindigan ba saboda ba su mutunta alƙawari, sannan ba su ɗauki ran ɗan Adam a bakin komai ba.
Asali: Legit.ng