Shugaba Tinubu Ya Aike da Sakon Ta'aziyyar Rasuwar Tsohon Minista a Kano
- Bola Ahmed Tinubu ya tura sakon ta'aziyya dangane da rasuwar tsohon minista kuma jigon APC, Sanata Bello Maitama Yusuf
- Shugaban ƙasa ya ce marigayin mutum ne mai garkiya da taimakon matasa kuma 'yan Najeriya ba zasu manta da shi ba
- Tinubu ya yi addu'ar Allah ya gafarta masa ya kuma bai wa iyalansa haƙurin jure wannan rashi da ba za a iya cike gurbinsa ba
FCT Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana matukar alhini kan rasuwar tsohon minista kuma babban jigo a jam’iyyar APC, Sanata Bello Maitama Yusuf.
Rahoton jaridar Vanguard ya tattaro cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwan ta'aziyya wadda mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Jumu'a.
Shugaban ƙasar ya kuma tura saƙon jaje da ta'aziyya ga iyalan marigayi Sanata Yusuf, 'yan uwa da abokan arziƙi, da kuma gwamnati da al'ummar jihar Jigawa baki ɗaya.
Bola Tinubu ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mutumin da ya yi imani na gaske da haɗin kan ƙasa, Sanata Maitama Yusuf ya bada gudummuwa mai yawa wajen haɓaka ƙasar nan, a ɓangaren hidima ga jama'a ba shi da son kai."
"Ya yi wa Najeriya aiki a matsayin minista a ma’aikatun harkokin cikin gida da kasuwanci na tarayya kafin al’ummarsa su zabe shi zuwa majalisar dattawan Najeriya."
"Ana girmama marigayin bisa fafutukar tabbatar da shugabanci nagari, gaskiya, da kuma baiwa matasa dama a lokacin da yake majalisar dattawa. Daga baya ya tsunduma cikin kasuwanci, kuma ya samu nasara."
Marigayin ya bada gudummuwa - Tinubu
Bugu da ƙari, shugaba Tinubu ya ce yan Najeriya za su jima suna tuna irin gudummuwar da marigayin ya bada wajen hana ƙara wa'adin zaɓaɓɓun shugabanni.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan Sardaunan Dutse ya sa ya huta, ya baiwa duk wadanda suka shiga ƙunci haƙuri bisa wannan rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba, Tribune ta ruwaito.
KWASU: Shugaba Bola Tinubu Ya Kuma Nada Dalibar Jami'a a Mukami
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya ƙara naɗa dalibar jami'a da ke karatun digirin farko a kwamitin tsare-tsaren kasafi da sake fasalin haraji.
Ya naɗa Olamide Obagbemileke, ɗalibar 400-Level da ke karatun tattalin arziki a jami'ar jihar Kwara a matsayin mai taimakawa kan bincike da nazari.
Asali: Legit.ng