Gwamnan Zamfara Ya Yi Watsi da Batun Yin Sulhu da Yan Bindiga

Gwamnan Zamfara Ya Yi Watsi da Batun Yin Sulhu da Yan Bindiga

  • Gwamnan jihar Zamfara ya sake nanata matsayarsa ta cewa gwamnatinsa ba za ta tattauna da ƴan bindiga ba
  • Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta tattauna da su ba saboda ba su ganin dararjar ran ɗan Adam
  • Lawal ya yi nuni da cewa idan ƴan bindigan na son a yi sulhu da su, dole ne su fito su ajiye makamansu

Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya jaddada matsayarsa ta cewa ba zai tattauna da ƴan bindiga ba, yana mai nanata cewa zai yaƙi ƴan bindiga har sai sun miƙa wuya.

Gwamnan yana mayar da martani ne a kan huɗubar Juma'a da wani mashahurin malami a jihar, Sheikh Ahmed Kanoma ya yi, wanda ya shawarci gwamnati da ta sake gwada hanyoyin sulhu domin samun zaman lafiya a jihar.

Kara karanta wannan

Ministan Birnin Tarayya Nyesom Wike Ya Bayyana Dalilin da Yasa Ya Yarda Ya Yi Aiki da Tinubu

Gwamna Dauda ya ce ba batun sulhu da yan bindiga
Gwamna Dauda ya ce ba zai tattauna da yan bindiga ba Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

A cewar rahoton The Punch, Kanoma ya shawarci gwamnatin jihar da ta sake gayyatar ɗaukacin shugabannin ƴan bindigan tare da zama da su domin samun dawwamammen sulhu kan matsalar tsaro a jihar.

Meyasa gwanmna Dauda ba zai yi sulhu da ƴan bindiga ba?

Sai dai, gwamna Lawal ya ce babu dalilin yin sulhu da mutanen da ba su cika alƙawari, kuma ba su ganin ƙimar rayuwar ɗan Adam.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Har yanzu ina kan matsayata ta rashin tattaunawa da ƴan bindiga kamar yadda na sanar a baya. Ta yaya za ku yi sulhu da wanda ya fita kashe mutane da sace mutane domin neman kudi? Sau nawa gwamnatocin baya suka yi sulhu da ƴan bindiga? Shin hakan yayi aiki?"

Sai dai, gwamnan ya bayyana cewa idan ƴan fashin na son a yi sulhu, to su fito daga daji su miƙa makamansu.

Kara karanta wannan

Kujerar Mataimakin Gwamnan APC Na Tangal-Tangal, Majalisa Ta Tabbatar da Shirin Tsige Shi

Ya kara da cewa:

"Idan suna son sulhu, to su miƙa makamansu, su fito domin tattaunawa. Idan ba su yi haka ba, zan bi su, in yaƙe su har sai sun daina. Ina sake maimaitawa, babu sulhu da wanda ba ya ganin darajar ran ɗan Adam."

Gwamnan ya yi kira ga ƴan siyasa da su daina siyasantar da matsalar tsaro, wacce ya bayyana a matsayin muguwar iska da ba za ta bar kowa ba.

Gwamna ya samu goyon baya

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin birnin Gusau, mai suna Jamilu Abdullahi, wanda ya nuna goyon bayansa kan matsayar gwamnan ta ƙin hawa teburin sulhu da ƴan bindiga.

Jamilu ya bayyana cewa sam ƴan bindiga ba mutanen da za a yin alƙawari da su ba ne, domin ko an yi ba su mutunta shi.

Ya nuna goyon bayansa kan a cigaba da ragargazarsu har sai an kawo ƙarshensu a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC a Arewa Ya Yi Fatali da Gargaɗin Gwamnatin Tinubu, Ya Haramta Muhimmin Abu 1 a Jiharsa

Yadda Aka Sace Daliban FGC Yauri

A wani labarin kuma, ɗaya daga cikin ƴan bindigan da suka sace ɗaliban makarantar FGC Yauri, ya bayyana yadda suka aikata wannan ɗanyen aikin.

Auwal Abdullahi ya ce Kachala Dogo Gide da wasu ƴan bindiga kusan 100 su ka dura makarantar gwamnatin, su ka yi garkuwa da yaran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng